2019: An ba Gwamnatin Buhari shawarar abin da za tayi a wannan karo

2019: An ba Gwamnatin Buhari shawarar abin da za tayi a wannan karo

Yayin da ake taya shugaba Muhammadu Buhari murnar sake lashe zaben Najeriya, mun ji labari cewa mutanen kasar sun soma ba shugaban na su shawarar irin gyaran da ya kamata yayi idan ya dawo kan mulki a karon sa na biyu.

2019: An ba Gwamnatin Buhari shawarar abin da za tayi a wannan karo
An yi amfani da kafofin sadarwa na zamani wajen ba Buhari shawararwari bayan ya ci zabe
Asali: Twitter

Daga cikin wadanda su ka bada na su shawarwarin akwai wani Mai suna ElTama 007 wanda yace akwai bukatar Buhari yayi abubuwa kamar haka

1. A kawo karshen satar jama’a da ake yi a Arewa.

2. Sannan kuma a farfado da tattalin arziki

3. Gwamnatin Buhari ta jawo kowa a jika.

4. Ayi yaki da cin hanci ba tare da la’akari da jam’iyya ba

5. A kuma sauya manyan mukarraban gwamnati

Shi kuma wani Rotimi Olawole wanda ke da kishin ilmi da cigaban matasa a Afrika cewa yayi ya kamata gwamnatin tarayya ta inganta karatun ‘ya ‘ya mata a fadin Najeriya. Wasu kuma su na so gwamnati ta duba lamarin auren wuri.

Dr. Ogbeni Dipo, wanda Malamin makaranta ne a kasar Turai, yana ganin akwai bukatar a tsige wasu Ministoci da su ka gaza irin su Adamu Adamu da Solomon Dalung, a cewar sa. United Baby kuma tana ganin a nada sabbabin Ministoci kurum.

KU KARANTA: Hukumar INEC ta ba Buhari takardar shaidar lashe zaben 2019

Yusuph Dauran da irin su Abdul Balarabe su na ganin ya kamata shugaban kasa Buhari ya duba halin da ake ciki a jihar Zamfara. Omosaro Ali kuma tana so ne a samar da wutan lantarki sannan Buhari ya kyale Aisha Buhari ta rika aiki da kyau,

Farouk Yola, wani ‘dan siyasa a Jihar Kano, yayi kira ga shugaban kasa Buhari ya waiwayi mutanen Arewacin kasar sannan kuma a binciki duk marasa gaskiya. Yola ya kuma nemi a nada Ministoci da wuri a soma aiki babu kaukautawa.

Ibrahim Aweda yayi kira ga shugaban kasa mai-ci ya maida hankalin sa da kyau wajen inganta ilmi, da samar da wutan lantarki kamar sauran kasashe da babbako da harkar kasuwanci da ya ruguje a Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel