An sake kwatawa: Yan bindiga sun yi garkuwa da babban basarake, sun kashe mutane 13 a Zamfara

An sake kwatawa: Yan bindiga sun yi garkuwa da babban basarake, sun kashe mutane 13 a Zamfara

Wasu gungun yan bindiga sun kai mummunan hari a kauyen Kawaye dake cikin karamar hukumar Anka ta jahar Zamfara, inda suka kashe mutane goma sha uku, a ranar Talata, 26 ga watan Feburairu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wani mazaunin kauyen daya tsallake rijiya da baya, Aliyu Muhammad wanda ya bayyana cewa yan bindigan sun shiga kauyen ne akan babura da yawa tare da bude ma jama’a wuta.

KU KARANTA: Yan bindiga sun bude ma magoya bayan Buhari wuta yayin da suke tsaka da murnar nasara

Aliyu yace yayin da suka sauka daga kan baburan nasu sai suka fara banka wuta ga motoci, babura, kekuna, shaguna, da sauran gidajen jama’a, sa’annan suka yi awon gaba da hakimin yankin da matarsa, da wasu mutane arba’in.

Shima kaakakin rundunar Yansandan jahar, SP Muhammad Shehu ya tabbatar da aukuwar lamarin, sa’annan ya tabbatar da mutuwar mutane goma sha daya a sanadiyyar harin da yan bindigan suka kai.

Amma kaakakin ya bayyana cewa rundunar ta tura jami’anta da suke aiki tare da dakarun Sojin Najeriya zuwa dazukan yankin domin ceto hakimin da matarsa da ma sauran mutanen da yan bindigan suka yi garkuwa dasu.

Haka zalika rundunar Yansandan jahar ta sha alwashin kama yan bindigan tare da duk masu daukan nauyinsu, daga karshe kuma yace a yanzu zaman lafiya ya koma yankin, sa’annan an baza jami’an tsaro don tsaurara matakan tsaro a jahar.

A wani labarin kuma, wasu gungun yan bindiga sun halaka jami’in dansanda mai mukamin kofur dake aikin bayar da tsaro ga sakamakon zabe tare da yi musu rakiya daga karamar hukumar Ipokia zuwa cibiyar tattara sakamakon zabe dake garin Ilaro na jahar Ogun.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel