Babban Lauyan Najeriya Agbakoba ya nemi Atiku ya rungumi kaddara

Babban Lauyan Najeriya Agbakoba ya nemi Atiku ya rungumi kaddara

Wani tsohon shugaban kungiyar Lauyoyin Najeriya na NBA watau Olisa Agbakoba, yayi kira ga ‘dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP, Alhaji Atiku Abubakar, da ya hakura da maganar zuwa kai kara a kotu.

Babban Lauyan Najeriya Agbakoba ya nemi Atiku ya rungumi kaddara
Olisa Agbakoba yace kabilanci ne yayi tasiri a zaben 2019
Asali: UGC

Olisa Agbakoba yana ganin cewa ya kamata Atiku Abubakar wanda ya gwabza da shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben da aka yi kwanan nan, ya ajiye batun zuwa kotun karar zabe domin kalubalantar nasarar APC.

Babban Lauya Olisa Agbakoba SAN yayi wannan bayani ne a wani jawabi da ya fitar jiya Laraba inda yace zaben ya nuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bai rasa farin jinin da yake da shi tun fil azal a yankin Arewa ba.

KU KARANTA: Manyan kasashen Afrika su na taya Buhari farin cikin lashe zabe

Cif Agbakoba yake cewa, haka-zalika, Atiku Abubakar ya samu nasara a Kudancin Najeriya. Gawurtaccen Lauyan yana ganin cewa kabilanci yayi tasiri a zaben, sai dai yana ganin cewa duk da haka ya kamata Atiku ya hakura.

Lauyan yake cewa ya san cewa ‘dan takarar na PDP ba zai ji dadin kayin da ya sha a hannun shugaba Muhammadu Buhari ba, inda yake zargin cewa an tafka magudi na kin-karawa a zaben. Agbakoba abin da ya fi shi ne PDP ta yi hakuri.

Tsohon shugaban na NBA yana ganin cewa gaba ta fi baya yawa, don haka kurum gara ‘dan takarar na PDP yayi halin girma ya amince da zaben, har kuma ya tattaro kan sauran kananan jam’iyyu domin su yi karfi har su nemi mulki a gaba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel