Jami’an ‘Yan Sanda sun maka Mutane 6 a kotu da zargin hargitsa taron APC

Jami’an ‘Yan Sanda sun maka Mutane 6 a kotu da zargin hargitsa taron APC

A jiya ne Jami’an tsaro na ‘yan sanda sun cafke mutanen da ake zargi da jifae tawagar shugaban kasa Muhammadu Buhari a lokacin da jirgin yakin neman zaben sa ya shigo jihar Ogun kwanakin baya.

Jami’an ‘Yan Sanda sun maka Mutane 6 a kotu da zargin hargitsa taron APC
An kama wadanda su ka rike jifar tawagar Shugaba Buhari a Ogun
Asali: Twitter

Rundunar ‘yan sandan Najeriya na jihar Ogun sun yi ram da wasu mutum 6 da ake tunani su na da hannu wajen kawo hatsaniya a taron kamfen din APC da aka yi a Garin Abeokuta da ke jihar Ogun a lokacin ana yakin neman zabe.

Daily Trust ta rahoto mana cewa jami’in ‘yan sandan da ke magana a madadin Rundunar jihar Ogun watau Abimbola Oyeyemi ya fitar da jawabi inda yace sun kama wandada su ka rika jifar mutanen shugaban kasa kwanakin baya.

KU KARANTA: Buhari ya fadawa Magoya bayan su da su guji tsangwamar 'Yan adawa

Mutanen da jami’an tsaro su ka kama a cikin ‘yan kwanakin nan su ne Olaoye Tunde (43); Bashiru Alli (40); Ayoola Muyiwa (50), Yakubu Wahab ( 28); Opeyemi Omiyefa (31) da kuma wani Bawan Allah mai suna Akeem Biliaminu (38).

Ana zargin cewa wadannan mutum 6 ne su ka rika jefawa jama’a duwatsu da wasu tarkace a lokacin da ake gangamin jam’iyyar APC mai mulki a cikin filin wasa na MKO Abiola International Stadium, da ke Garin Kuto a babban birnin Ogun.

Yanzu dai an mikawa kotu wadannan mutane inda ake shirin yanke masu hukunci. DSP na 'Yan Sanda Abimbola Oyeyemi, a madadin jami’an tsaro na jihar, yace za a dauki matakin da ya dace a kan mutanen.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel