Yan bindiga sun bude ma magoya bayan Buhari wuta yayin da suke tsaka da murnar nasara

Yan bindiga sun bude ma magoya bayan Buhari wuta yayin da suke tsaka da murnar nasara

Wasu gungun yan bindiga a ranar Laraba 27 ga watan Feburairu sun bude ma taron masoya shugaban kasa Muhammadu Buhari wuta yayin da suka tsaka da bikin murnar samun nasarar da Buhari yayi a zaben shugaban kasa.

Wannan lamari mai matukar muni ya faru ne a daidai layin Iyawa a unguwar Sabo dake yankin Yaba na jahar Legas, inda yan bindigan suka tarwatsa taron magoya bayan Buharin bayan sun bude musu wuta, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Ahmed Musa ya taka rawar murnar nasarar shugaba Buhari

A sanadiyyar haka mutum guda ya rasa ransa nan take, yayin da wasu da dama suka jikkata, kamar yadda kaakakin rundunar Yansandan jahar, Chike Oti ya tabbatar. Sai dai Kaakaki Oti yace a wani labari kuma, wasu matasan dake murnar nasarar Buhari sun far ma Yansanda, sun jikkata guda daya.

Kaakakin yace wasu matasa sun lakada ma jami’in Dansanda dan banzan duka akan babbar hanyar Badagry a lokacin da Yansandan suka yi kokarin janyo hankalin matasan game da tare hanyar da suka yi, wanda ya janyo cunkoson ababen hawa akan hanyar.

“Daga wannan magiyar ne fa sai matasan suka far musu da adduna da sanduna inda suka diran ma wani DCO har sai daya fadi sumamme, duk mun dauka ya mutu, amma daga bisani ya farfado bayan DPO yasa an mikashi zuwa Asibiti.” Inji shi.

Kaakaki Oti yace kwamishinan Yansandan jahar Legas, Zubairu Muazu ya gargadi jama’a cewa rundunar ba zata lamunci cin zarafin jami’anta ba, musamman a lokacin da suke gudanar da aikinsu kamar yadda doka ta tanada.

Daga karshe rundunar ta bayyana cewa ta kama mutane talatin da bakwai dake hannu cikin kai ma Yansandan hari, kuma a yanzu haka ta kaddamar da bincike akansu, haka zalika yansanda sun yi alkawarin kamo dan bindigan daya kashe masoyin Buhari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel