Mun yanka Shugaban Majalisa Saraki mun bizne a siyasa – Oshiomhole

Mun yanka Shugaban Majalisa Saraki mun bizne a siyasa – Oshiomhole

Shugaban jam’iyyar APC na kasa baki daya watau Kwamred Adams Oshiomhole, ya bayyana cewa sun kashe siyasar Bukola Saraki wanda shi ne shugaban majalisar tarayyar Najeriya a halin yanzu.

Mun yanka Shugaban Majalisa Saraki mun bizne a siyasa – Oshiomhole
Adams Oshiomhole yace babu Saraki babu kayan sa a siyasa
Asali: UGC

Adams Oshiomhole yake cewa sun kashe Bukola Saraki, kuma har sun bizne sa a siyasa. Shugaban jam’iyyar APC din ya bayyana wannan ne lokacin da yake magana da manema labarai a fadar shugaban kasa jiya a Garin Abuja.

Shugaban APC na kasa yake cewa wadanda su ka samu zuwa majalisa da yawan kuri’un da ba su haura 100, 000 ba sun hana ruwa gudu a gwamnatin nan. Oshiomhole yake cewa Allah yayi yanzu wadannan mutane sun sha kashi.

KU KARANTA: APC tana zargin Gwamnan ta da laifi wajen samun nasarar Atiku

Duk da shugaban na APC bai kama suna ba, bayanin sa ya nuna cewa yana magana ne a kan Bukola Saraki wanda aka tika da kasa a makon da ya gabata. Saraki ya rasa kujerar sa ta Kwara ta tsakiya ne a hannun Ibrahim Oloriegbe.

Kwamared Oshiomhole yake cewa yayin da ake batun tsige shi (Bukola Saraki) a majalisar dattawa, sai ga shi mutanen yankin sa na Kwara sun lallasa sa a zaben da aka yi. Oshiomhole yace wannan ya nuna karfin damukaradiyya.

Babban shugaban na APC yake cewa duk rikar mutum a siyasa, yanzu an gane cewa bai kamata yayi wasa da Talakawan sa ba domin kuwa za su iya tika sa da kasa, idan har ba ya yin abin da su ke so kamar yadda aka yi a bana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel