Kungiyar Matasan Ibo ta bayyana dalilin da ya sanya ta yi goyon bayan Buhari a zaben 2019

Kungiyar Matasan Ibo ta bayyana dalilin da ya sanya ta yi goyon bayan Buhari a zaben 2019

Babbar kungiyar matasan Kabilar Ibo ta Ohanaeze Ndigbo Youth Council, ta bayyana dalilin da ya sanya ta zage dantse wajen goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin babban zaben kasa da aka gudanar a makon da ya gabata.

Kungiyar ta Ohanaeze ta ce ta yi watsi da dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, duba da amincin dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar APC da ke da tsare-tsare na cikar burikan al'ummar kabilar Ibo.

Shugaban kasa Buhari yayin yakin zaben sa a jihar Bayelsa
Shugaban kasa Buhari yayin yakin zaben sa a jihar Bayelsa
Asali: Facebook

A yayin da kungiyoyi da kabilu da dama a fadin kasar nan suka bayyana goyon baya tare da zabin 'yan takara ta fuskar shimfidar aminci a gare su, kungiyar Ohanaeze ta ce ta yi dogon nazari wajen bayyana amincin ta ga shugaban kasa Buhari domin 'yan kabilar Ibo su ci moriya mai girman gaske.

Jagoran kungiyar, Okechukwu Isiguzoro, shine ya bayar da shaidar hakan cikin wata hira yayin ganawa da manema labarai a jiya Asabar cikin birnin Abakaliki na jihar Ebonyi da ke Kudancin kasar nan.

KARANTA KUMA: Atiku ya nemi Kotu ta bayar da umarnin sake gudanar da babban zabe

Isiguzoro ya ce Atiku ya nemi takarar kujerar shugaban kasa da manufa ta kyautatawa al'umma da kuma yankin Arewacin kasar nan inda ya yi yunkurin ribatar abokin takarar sa, Peter Obi, domin samun goyon bayan yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

A yayin babban zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019, shugaban kasa Buhari ya yi nasara inda ya lallasa babban abokin adawar sa da gamayyar kuri'u ta fiye da miliyan uku.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel