Atiku ya nemi Kotu ta bayar da umarnin sake gudanar da babban zabe

Atiku ya nemi Kotu ta bayar da umarnin sake gudanar da babban zabe

Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, a jiya Asabar ya kaddamar da kungiyar lauyoyin sa domin kalubalantar sakamakon babban zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, kungiyar lauyoyin bisa jagorancin Dakta Livy Uzoukuwa (SAN), za ta kalubalanci sakamakon babban zaben ta hanyar neman kotu ta yi watsi da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Atiku ya nemi Kotu ta bayar da umarnin sake gudanar da babban zabe
Atiku ya nemi Kotu ta bayar da umarnin sake gudanar da babban zabe
Asali: UGC

Majiyar rahoton da ke da kusanci ga Atiku da kuma shugabancin jam'iyyar sa ta PDP ta ruwaito cewa, kungiyar Lauyoyin za ta nemi kotu ta yi shela tare da bayyana Wazirin Adamawa a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar shugaban kasa da aka gudanar a makon da ya gabata.

A madadin haka, kungiyar lauyoyin bisa ga madogara ta dalilai da kuma hujjoji za ta bai wa kotu zabi na bayar da umarnin sake gudanar da babban zaben kasa domin tabbatar da nasarar tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya.

A ranar Larabar da ta gabata ne hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC, yayin zayyana sakamakon babban zaben kasa ta bayyana nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin ya lashe zaben kasa na ranar Asabar.

KARANTA KUMA: Yadda Buhari ya yi nasara a zaben 2019 - Ra'ayi

Biyo bayan wannan hukunci Atiku ya bayyana rashin amincewar sa kai tsaye tare da wassafa wasu dalilai na murdiya gami da magudi da kuma miyagun ababe na rashin gaskiya da adalci da suka auku da manufa ta rinjayar da nasara ga jam'iyyar APC yayin babban zaben.

Yayin misalta zaben da ya gudana a matsayin mafi munin zabe da ya auku a tarihin kasar nan, Atiku tare da shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus, a halin yanzu sun lashi tsinin takobi da cewar hakan ba za ta sabu ba domin kuwa za su ribaci kotun shari'a wajen neman hakkin su.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel