Yadda Buhari ya yi nasara a zaben 2019 - Ra'ayi

Yadda Buhari ya yi nasara a zaben 2019 - Ra'ayi

Biyo bayan lashe kuri'u 15, 191,847 da suka tabbatar da nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin babban zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar ta makon da ya gabata, alkalumma sun yi hasashen dalilai na samun nasarar sa.

Samun kuri'u 3,928,969 doriya akan kuri'un da babban abokin adawar sa ya samu, Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP, hukumar zabe ta kasa a jiya bayan kammala kidayar kuri'u ta tabbatar da nasarar shugaban kasa Buhari.

Shugaban kasa Buhari yayin yakin zaben sa a jihar Kano
Shugaban kasa Buhari yayin yakin zaben sa a jihar Kano
Asali: Depositphotos

Alkalumma sun yi hasashen cewa, shugaban kasa Buhari ya taka mataki na sa'a wajen samun nasara a sanadiyar gagarumin goyon baya da ya samu daga yankunan Arewa maso Yamma, da kuma babban kaso na sassan yankunan Arewa maso Gabashin Najeriya.

Kazalika shugaban kasa Buhari ya yi galaba akan sauran 'yan takarar kujerar shugaban kasa cikin yankunan Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Yamma, baya ga goyon baya da ya samu daidai gwargwado a yankunan Kudu maso Gabas da kuma Kudu maso Kudu duk da kasancewar su cibiyoyi na jam'iyyar adawa ta PDP.

Masu sharhi akan harkokin siyasa sun bayyana cewa, baya ga farin jini, kwazon Buhari a yankunan Arewa musamman ta fuskar nadin mukamai masu tsoka ya taka rawar gani wajen samun nasarar sa a yankin.

KARANTA KUMA: Nasarar Buhari ta tayar da tarzoma a garin Legas, Oyo, Abuja

Da dama daga cikin al'ummar Arewa sun gaza zaben Atiku a sanadiyar akidar sa ta sauya fasalin kasa da kuma sha'awar da ya nuna akan yankunan Kudu da a cewar su hakan zai janyo wa yankunan su na Arewa koma baya da ya sanya suka kadawa shugaba Buhari kuri'un su a yayin babban zabe.

Kazalika, hasashen ya bayyana cewa, jam'iyyar APC ta samu goyon baya a yankunan Kudu maso Gabas da kuma Kudu maso Yamma sakamakon hankoron cin gajiyar kujerar shugaban kasa Buhari a zaben 2023.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel