Sakamakon Zabe: PDP na shirin tayar da bore a Najeriya

Sakamakon Zabe: PDP na shirin tayar da bore a Najeriya

A bisa mahanga ta fahimta da kuma bincike, jaridar The Nation ta gano cewa akwai kitimurmura da jam'iyyar adawa ta PDP ke shiryawa da manufa ta kawo hargitsi gami da yiwa sakamakon babban zaben kasa bore.

Duk da cewa jam'iyyar PDP ta zabi neman hakkin ta gaban hukumomi na shari'a dangane da sakamakon babban zabe da aka gudanar a ranar Asabar ta makon da ya gabata, binciken jardar The Nation ya tabbatar da cewa akwai wani tuggu da ta kulla na daban.

Binciken ya gano cewa, jiga-jigan jam'iyyar PDP sun shirya yiwa sakamakon zabe bore da nuna rashin amincewar su ta hanyar neman hadin gwiwar wasu kungiyoyi a nan gida na Najeriya da kuma kasashen ketare domin aiwatar da zanga-zanga mai girman gaske.

Sakamakon Zabe: PDP na shirin tayar da bore a Najeriya
Sakamakon Zabe: PDP na shirin tayar da bore a Najeriya
Asali: Depositphotos

Ana zargin wani tsohon shugaban kasa da kuma tsaffin manyan dakarun soji na da hannu dumu-dumu cikin wannan kitimurmura ta yiwa sakamakon zabe bore kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.

Wannan shiri da aka kulla yayin wani zaman ganawa na gaggawa ya biyo bayan gazawar jam'iyyar PDP wajen hana hukumar zabe ci gaba da bayyana sakamakon babban zaben kasa a daren ranar Talata.

KARANTA KUMA: Masu tayar da zaune tsaye a jihar Sakkwato, Kaduna su kuka da kansu - Buhari

Yayin da majiyar rahoton ta hukumar ta bukaci a sakaya sunan ta, ta kuma bayyana cewa, wannan shiri na ci gaba bisa ga jagorancin dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, da kawowa yanzu ya tubure akan rashin amincewa da sakamakon zaben.

Majiyar ta kara da cewa, PDP na ci gaba da kulla kitimurmura ta tayar bore a fadin kasar nan tare da hadin gwiwar kungiyoyi da suka hadar da; Ohanaeze, Afenifere, Middle Belt Forum, kungiyoyi Mata da kuma Dalibai.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel