Sakamakon zabe: Mun san adadin kuri’u na gaskiya da mu ka samu – Atiku

Sakamakon zabe: Mun san adadin kuri’u na gaskiya da mu ka samu – Atiku

Atiku Abubakar, dan takarar neman zama shugaban kasar Najeriya a karkashin inuwar jam’iyyar PDP a zaben da aka yi ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu, ya cigaba da sukar sakamakon zaben da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana.

Da duku-dukun safiyar ranar Laraba, 27 ga watan Fabarairu, ne INEC ta bayyana cewar shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ne ya lashe zaben kujerar shugaban kasa.

Da ya ke sanar da sakamakon zaben, Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban INEC, y ace Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 15,191,847 da su ka bashi nasara a kan abokin hamayyar sa, Atiku Abubakar, na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 11,255,978.

A wani jawabi da ya fitar bayan shugaban INEC ya bayyana sakamako, Atiku y ace akwai alamun tambaya a kan sakamakon zaben tare da ikirarin cewar zai kalubalance shi a kotu.

Sakamakon zabe: Mun san adadin kuri’u na gaskiya da mu ka samu – Atiku
Atiku
Asali: Facebook

A wani taro da ya yi da manema labarai na duniya a Abuja, Atiku ya bayyana sakamakon zaben da cewar ‘fashi’ ne ga zabin ‘yan Najeriya.

A cewar sa, alkaluman da INEC ta bayyana a sakamakon zaben ba daidai ba ne.

Atiku y ace: “mu na da alkaluman sakamakon zabe na gaskiya, mu na kuma da bayanai a kan yadda aka gudanar da zaben ranar 23 ga watan Fabrairu.

DUBA WANNAN: Nasarar Buhari: Fayose ya yaba wa ‘yan Najeriya, ya yi ma su albishir

Ba wai ina magana ne a matsayin dan jam’iyyar PDP ba. Ina Magana ne a matsayin dan Najeriya da gwamnatin Buhari ta yi wa fashin nasara a zaben da aka yi ranar Asabar. Sakamakon da aka bayyana ba shine abinda ‘yan Najeriya su ka zaba ba.

“A saboda wannan dalili ne ni, Atiku Abubakar, na ki amincewa da sakamakon da INEC ta bayyana a kan cewar Muhammadu Buhari ne ya lashe zabe ta hanyar samun haramtattun kuri’u ma fi rinjaye,” a kalaman Atiku.

Atiku ya kara da cewa a tsawon shekaru fiye da 30 da ya yi ya na siyasa bait aba ganin lalataccen zabe irin wanda INEC ta gudanar ranar Asabar da ta gabata ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel