Ruwa-a-jallo: Buba Galadima ya bayyana a bainar jama'a bayan nasarar Buhari

Ruwa-a-jallo: Buba Galadima ya bayyana a bainar jama'a bayan nasarar Buhari

Buba Galadima ya bayyana a cibiyar tuna wa da Shehu Musa 'Yar Adua a Abuja, inda Atiku Abubakar zai yi wa manema labarai jawabi ranar Laraba.

A karshen makon jiya ne dan siyasar ya yi batan-dabo, kamar dai yadda majiyoyin mu suka ruwaito.

A ranar Lahadi ne iyalan Buba Galadima suka tabbatar wa da daya daga cikin majiyoyin mu cewa suna zargin jami'an tsaron farin kaya ne na DSS suka kama dan siyasar da rana jim kadan bayan ya fita daga gidansa.

Ruwa-a-jallo: Buba Galadima ya bayyana a bainar jama'a bayan nasarar Buhari
Ruwa-a-jallo: Buba Galadima ya bayyana a bainar jama'a bayan nasarar Buhari
Asali: UGC

KU KARANTA: Dalilan Atiku 5 na kin amincewa da sakamakon zaben 2019

Sai dai da wakilin gidan labaran BBC ya tambaye shi ko ina ya shige sai shi Injiniyan ya kada baki ya ce ba zai yi magana a kan sa ba lokacin domin harkar dake gaban sa ta zabe ce sai a wani lokaci nan gaba zai bayar da karin haske.

A kwanan baya ma dai kakakin yakin neman zaben Atiku Abubakar din watau Buba Galadima ya gamu da iftila'in hadarin mota. Lamarin ya faru ne kan hanyar Hadeja zuwa Kano a yammacin ranar.

Wani makusancin jagoran Alhaji Sabo Imamu Gashau wanda suke tare a cikin motar lokacin da lamarin ya faru ya ce ba bu wani da ya ji mumunan rauni bayan aukuwar hadarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel