Adam A Zango ya taya Buhari murnar lashe zabe a karo na biyu (bidiyo)

Adam A Zango ya taya Buhari murnar lashe zabe a karo na biyu (bidiyo)

Shahararren dan was an nan na Kannywood kuma mawakin zamani, Adam A Zango ya taya Shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar lashe zaben Shugaban kasa a karo na biyu a zaben da ya gudana a ranar Asabar da ya gabata.

A wani dan gajeran bidiyo da jarumin ya wallafa a shafinsa na Facebook ya nuna farin ciki akan nasarar da Shugaban kasar yayi inda har ya ajiye lemun kwalba a gabansa domin bikin wannan nasara.

Hakan na zuwa ne dai bayan jarumin ya bar tafiyar Baba Buhari inda ya koma tafiyar Atiku Abubakar dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar PDP.

Wannan sauyin sheka da jarumin yayi ya haddasa cece-kuce da kawo masa bakin jini a wajen wasu mutane da dama, lamarin da ya tursasa shi barin shafin zumunta na Instagram.

KU KARANTA KUMA: APC ta lashe kujerar Sanata a Bauchi ba tare da dan takara ba

Sai kuma gashi a yanzu ya dawo da murna harma da farin ciki kan nasarar Buhari yana mai cewa “Assalamu alaikum warahmatullahi ta’ala wa barkatuhu. Ina taya mai girma Shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar lashe zabe a karo na biyu wato ma’ana Next Level 4+4 Ubangiji Allah ya taya ka riko Baba, Allah ya sa ka gama mulkin ka lafiya, chas for Baba Buhari.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel