Kar ku tsangwami ‘yan jam’iyyar adawa – Rokon Buhari ga masoya da mgoya bayan sa

Kar ku tsangwami ‘yan jam’iyyar adawa – Rokon Buhari ga masoya da mgoya bayan sa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki masoya da magoya bayansa da kar su tsangwami ko ci mutuncin ‘yan jam’iyyar adawa yayin da su ke murnar nasarar da ya samu ta lashe zaben kujerar shugaban kasa a karo na biyu.

A jawabin godiya da ya yi a ofishin yakin neman zabensa na kasa da ke Abuja, Buhari, ya yi godiya ga duk wadanda su ka bayar da gudunmawar wajen samun nasarar sa.

Da ya ke sanar da sakamakon zaben, Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban INEC, ya ce Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 15,191,847 da su ka bashi nasara a kan babban abokin hamayyar sa, Atiku Abubakar, na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 11,255,978.

Kar ku tsangwami ‘yan jam’iyyar adawa – Rokon Buhari ga masoya da mgoya bayan sa
Buhari
Asali: Facebook

A wani jawabi da ya fitar bayan shugaban INEC ya bayyana sakamako, Atiku y ace akwai alamun tambaya a kan sakamakon zaben tare da ikirarin cewar zai kalubalance shi a kotu.

DUBA WANNAN: Nasarar Buhari: Fayose ya yaba wa ‘yan Najeriya, ya yi ma su albishir

Bayan ya yi godiya ga shugabancin jam’iyyar APC, da jagoranta na kasa, Bola Tinubu, mambobin kwamitin yakin neman zabensa da masoya da magoya baya da dukkan wadanda su ka bayar da gudunmawa, shugaba Buhari ya kara da cewa, “ina son na yi roko na musamman ga magoya baya na da kada su tsangwami ko ci mutucin ‘yan jam’iyyar adawa. Nasarar da na samu kadai ta isa zama sakayya ga kokarin ku.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel