Zaben 2019: Dalilain Atiku 5 na kin amincewa da nasarar Buhari

Zaben 2019: Dalilain Atiku 5 na kin amincewa da nasarar Buhari

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, wato Atiku Abubakar ya yi watsi da sakamakon zaben da hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC ta sanar, inda ya ce; zai kalubalanci sakamakon a kotu nan ba da dadewa ba.

Atiku ya bayyana hakan ne a takardar da ya sakawa hannu a yau Laraba ya kuma fitar a birnin tarayya Abuja. Inda ya ce; a bayyane yake cewa an yi murdiya a sakamakon zaben wadansu jihohin kasarnan. INEC dai ta ce; shugaba Buhari ne ya lashe zaben shugabancin kasar da aka yi.

Zaben 2019: Dalilain Atiku 5 na kin amincewa da nasarar Buhari
Zaben 2019: Dalilain Atiku 5 na kin amincewa da nasarar Buhari
Asali: Twitter

KU KARANTA: Rarara ya saki sabuwar wakar nasarar Buhari

Legit.ng Hausa ta fahimci ba kowa ne ya san ainihin hakikanin dalilan da dan takarar na PDP ya bayar ba da har yake ganin an yi murdiya a zaben shi yasa ma muka tattaro wasu dalilan da ya bayar a takardar da ya fitar:

1. Atiku yace abin mamaki ne a ce jihohin da suke cikin tashin hankali da rashin natsuwa a ce sun fi jihohin da suke cikin kwanciyar hankali fitowa zabe.

2. Atiku yace jami'an tsaro sun tarwatsa gudanar da zabe a wadansu rumfunan zabe da PDP ke da karfi a jihar Legas, Akwa-Ibom, Ribas da wadansu Jihohin.

3. Haka zalika Atiku yace a wasu jihohin irin su; Ribas, Akwa Ibom da Imo an yi amfani da karfin Soja, inda suka harbi mutane wadanda ya kamata a ce sun kare rayukansu.

4. Atiku yace ta ya ya za a ce kuri’un da ya samu a Akwa-Ibom, bai wuce kashi 50 ba kasa da yadda yake a 2015.

5. Atiku ya ce jami'an tsaro sun nuna rashin kwarewa sosai yayin zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel