Ya haura musu katanga don sata, yanzu zai zauna a kurkuku ko ya biya ninkin abin da ya sata

Ya haura musu katanga don sata, yanzu zai zauna a kurkuku ko ya biya ninkin abin da ya sata

- Kotu ta yankewa wani dan shekara 23 hukuncin wata 6 a gidan kaso

- An kamashi da laifin haura gidan mutane yayi sata

- An bashi zabin biyan tara ta N60,000

Akalla mutum 30 'yan PDP ne suka rasu a hadurruka daban-daban a yau
Akalla mutum 30 'yan PDP ne suka rasu a hadurruka daban-daban a yau
Asali: UGC

Kotu ta yankewa wani mutum dan shekara 23 hukuncin zama a gidan kaso na tsayin watanni 6 bisa laifin haura gidan mutane yayi sata,kiyasin abinda ya sata yakai N135,000.

Mai shari'a Mr Oke Obaleye dake zaman sa a kotun magistrate dake Abeokuta ya zartarwa Isma'il Ayo wannan hukunci ne bisa laifuka Biyu sata da kuma haura gidan mutane.

Wanda ake tuhumar ya amsa laifin sa ba tare da wani jinkiri ba.

Saboda hakane ya yanke masa zaman gidan kaso na tsayin watanni 6 ko kuma ya biya tara ta N60,000.

Insp Matthew Famuyiwa ya bayyanawa kotu cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne a ranar 17 ga watan Nuwamba shekara ta 2018 a Obada Oko wani yanki a Abeokuta.

GA WANNAN: An kama wata malama da laifin fyade ga wata yarinya a jihar Ikko

Famuyiwa ya kara da cewa wanda ake zargin ya shiga gidan wani mutumin ne mai suna Mr Ekundayo Boboye inda ya saci waya kirar Samsung S5 wadda kudinta yake N120,000 da kuma agogon hannu wanda yake N15,000 idan aka tattara kudin abubuwan daya sata ya kama N135,000.

Wannan laifi ya sabawa doka mai lamba 411 da kuma mai lamba 390(9) na dokokin jihar Osun 2016.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel