Ku amince da rashin samun nasara - Gwamna Abubakar ya shawarci Atiku da PDP

Ku amince da rashin samun nasara - Gwamna Abubakar ya shawarci Atiku da PDP

Gwamna Mohammed Abubakar na jihar Bauchi ya yi kira da dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP da ya sha kaye, Alhaji Atiku Abubakar ya amince da sakamakon zaben 2019 da kyakyawar zuciya.

Abubakar ya yi wannan kiran ne a ranar Laraba a jihar Bauchi a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai taimaka masa a fanin yada labarai, Abubakar Al-Sadique.

Ya kuma yi kira ga Atiku da jam'iyyar PDP su goyi bayan gwamnati mai zuwa domin ganin an samu nasarar ciyar da Najeriya gaba.

DUBA WANNAN: Yadda Buhari ya yi murdiyya wajen lashe zaben 2019 - Sheikh Ahmad Gumi

Ka amince da kayen da ka sha - Gwamna Abubakar ya fadawa Atiku da PDP
Ka amince da kayen da ka sha - Gwamna Abubakar ya fadawa Atiku da PDP
Asali: Depositphotos

"Demokradiya ikon Allah ne da ke wanzuwa ta hanyar kada kuri'un zabe.

"Saboda haka ina kira ga jam'iyyar adawa ta amince da kayen da ta sha ta kuma tallafawa sabon shugaban kasa da ya lashe saboda akwai wata zaben da za a ayi a nan gaba.

"Muna mika godiya ga Allah da ya kaddara aka gudanar da zaben cikin lafiya.

"Shugaba Muhamamdu Buhari yana da kyakyawar niyya ga Najeriya kuma zaben wannan shekarar alama ce da ke nuna al'ummar Najeriya sun amince da tsarin canji na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

"Zaben ya tabbatar da cewa shugaban kasa da Najeriya na kan turba mai kyau na sauya kasar," inji Gwamnan.

Gwamnan ya yi mubaya'a ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari inda ya yi kira ga al'ummar jihar su fito kwansu da kwarkwata domin kada kuri'a a zaben gwamna da 'yan majalisun siyasa na ranar 9 ga watan Maris kamar yadda NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel