Nasarar Buhari: Fayose ya yaba wa ‘yan Najeriya, ya yi ma su albishir

Nasarar Buhari: Fayose ya yaba wa ‘yan Najeriya, ya yi ma su albishir

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce ‘yan Najeriya ne su ka cancanci yabo bisa kwarin gwuiwar da su ka nuna yayin zaben shugaban kasa da ‘yan majalisar tarayya da aka yi ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

Fayose ya bayyana hakan ne a yau, Laraba, a wani jawabi da mai taimaka ma sa bangaren yada labarai, Lere Olayinka, ya fitar.

A cewar tsohon gwamnan, “sabanin yi wa shugaba Buhari murna, mutumin da zai mulki kasar mu bada son ran mu ba, ‘yan Najeriya ya kamata a jinjinawa bisa karfin guiwar da su ka nuna.

Ya bayyana rawar da hukumar zabe ta kasa (INEC) da hukumomin tsaro su ka taka a matsayin abin kunya, ya na mai kari da cewar tun farko da ma sun nuna niyyar su ta hana Najeriya samun shugabanci nigari.

Nasarar Buhari: Fayose ya yaba wa ‘yan Najeriya, ya yi ma su albishir
Fayose
Asali: Twitter

Yau a Najeriya da bakin bindiga ake kwatar zabe. Babu wanda ya ke murna da abinda ya faru sai wanda su ke amfana kai tsaye daga gwamnatin, wadanda su ka zabi tabbatar da biyan bukatar su ta hanyar hana ‘yan Najeriya abinda su ke so.

“Wannan zabe zai cigaba da zama a cikin bakin littafin tarihi saboda fyade ne ga tsarin dimokradiyya.

DUBA WANNAN: Murnar samun nasara: Gwamoni da jiga-jigan 'yan APC sun ziyrarci Buhari, hotuna

“Sabanin yin murna a wannan rana, ina mai jajanta wa ‘yan Najeriya, musamman wadanda su ka rasa ‘yan uwan su da wadanda su ka samu raunuka yayin zaben ranar Asabar,” a cewar Fayose.

Tsohon gwamnan ya kara da cewa, “ban a tsoron kamu ko dauri. Babu irin muzgunawar da ba a yi min ba saboda yadda na ke tsage gaskiya a kan gwamnatin tarayya.”

“Ina mai yaba wa ‘yan Najriya tare da yi ma su albishir din cewar kar su karaya, sauki na nan tafe watarana.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel