ACF ta bukaci Atiku da ya amince da burin mutane, ya taya Buhari murna

ACF ta bukaci Atiku da ya amince da burin mutane, ya taya Buhari murna

Kungiyar matasan Arewa wato Arewa Consultative Forum (ACF) ta yi kira ga dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben Shugaban kasa da aka kamala kwanan nan, Atiku Abubakar da ya amince da zabin mutane ta hanyar amsar kaye sannan ya taya Shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar samun nasara.

A wani jawabi dauke da sa hannun sakataren labaran kungiyar, Muhammad Ibrahim Biu, a ranar Laraba a Kaduna ya bayyana cewa Atiku a matsayinsa na dan damokradiyya wanda ke son zaman lafiyar damokradiyya toh kamata yayi ya amshi kaye musamman da yake akwai hujja da ke nuni da anyi zabe cikin lumana, gaskiya da kuma amana.

ACF ta bukaci sauran yan takara da nuna girma wajen amsar kaye ta hanyar taya abokin takararsu murna sannan su roki yan Najeriya da suma su yi bajintar da suka yin a jajircewa a zaben gwamna da na yan majalisar jiha.

ACF ta bukaci Atiku da ya amince da burin mutane, ya taya Buhari murna
ACF ta bukaci Atiku da ya amince da burin mutane, ya taya Buhari murna
Asali: UGC

Kungiyar ta taya shugaba Buhari nasarar sake lashe zabe a matsayin Shugaban Najeriya sannan sun jinjinawa kokarin Atiku Abubakar a zaben Shugaban kasar.

KU KARANTA KUMA: APC ta lashe kujerar Sanata a Bauchi ba tare da dan takara ba

Ta kuma yi kira ga shugaba Buhari da ya tabbatar da cewar sabuwar gwamnatinsa ta cika alkawaran da ta dauka na karfafa gwamnati saboda kada wani bangare ta ga an nuna mata wariya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel