Matakan da Atiku ke dauka ya zuwa yanzu, bayan ya sha kaye a hannun shugaban kasa Buhari

Matakan da Atiku ke dauka ya zuwa yanzu, bayan ya sha kaye a hannun shugaban kasa Buhari

- Dan takarar shugaban kasa a jam'iyar PDP yace yana jin kamshin nasara idan suka shiga kotu

- Zaben shekara ta 2019 shine zabe mafi muni a Najeriya

- Magudin zabe bazai samarwa da mutane gwamnati ba kuma wannan dalilin ne yasanya ban yadda da sakamakon ba.cewar Atiku

Matakan da Atiku ke dauka ya zuwa yanzu, bayan ya sha kaye a hannun shugaban kasa Buhari
Matakan da Atiku ke dauka ya zuwa yanzu, bayan ya sha kaye a hannun shugaban kasa Buhari
Asali: UGC

Dan takarar shugaban kasa a jam'iyar PDP Atiku Abubakar yace yanajin kamshi nasara a tare dashi a lokacin da suka shiga kotu.

Atiku ya bayyana inkarin sa akan sakamakon zaben inda yace shine zabe mafi muni a aka tabayi a Najeriya.

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya doke Atiku da kuri'u sama da miliyan Uku.

Da yake jawabi a wajen taron daya hada a ranar Laraba a Abuja Atiku ya bayyana wannan zabe a matsayin"implementation of grant theft of the people's will".

Yace an murkushe kuri'a a Akwa Ibom inda yace an samu ragin 62% na kuri'un da aka kada idan aka hada da na shekara ta 2015.

A jihar Borno kuma an samu karin 82% duba da rashin tsaro da aka samu a jihar.

Magudin zabe bazai samarwa da al'umma gwamnati ba kuma wannan shine dalilin rashin amince ta bisa sakamakon da aka fitar.

Atiku ya kara da cewa yana neman shawarar jam'iya da kuma yan Najeriya zuwa mataki na gaba.

Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben da ya gabata, yace ya tabbatar da cewa zai yi nasara a kotu.

Atiku yayi alkawarin cewa zai kalubalanci sakamakon zabe wanda ya kwatanta da "mafi muni" a tarihin damokaradiyyar Najeriya.

GA WANNAN: Majalisar dattijai ta dawo, ko dattijo Saraki ya sami halarta?

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC ya kada Atiku da sama da kuri'u miliyan uku.

A yayin jawabi ga taron manema labarai a Abuja a ranar laraba, Atiku yace zaben ya fuskanci "tabbatarwar sace ra'ayin mutane."

Yace takurawa masu saka kuri'u ya faru a jihar Akwa Ibom, kamar yanda yace, an samu kashi 65 na raguwar mutanen da suka saka kuri'a idan aka danganta da na 2015.

Yace a yayin da aka samu raguwa a Akwa Ibom, wacce jihar PDP ce, "Borno ta samu karin kashi 82 na karuwar kuri'un da aka saka duk da matsalolin tsaro dake jihar."

"Damfarar zabe bazata haifar da gwamnatin mutane ba saboda ba ta nuna ra'ayin mutane,"

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel