Murnar samun nasara: Gwamoni da jiga-jigan 'yan APC sun ziyrarci Buhari, hotuna

Murnar samun nasara: Gwamoni da jiga-jigan 'yan APC sun ziyrarci Buhari, hotuna

- Gwamnonin APC da shugabanni da jiga-jigan jam'iyyar sun ziyarci Buhari a fadar shugaban kasa domin taya shi murnar nasarar lashe zabe

- Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 15,191,847 da su ka bashi nasara a kan Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 11,255,978

- Shugaban hukumar zabe (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya sanar da sakamakon zaben da misalin karfe 4:28 na safiyar Laraba

Gwamnoni, shugabanni da ragowar wasu jigaigan 'ya'yan jam'iyyar APC sun ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa domin taya shi murnar samun nasarar sake lashe zaben kujerar shugaban kasar Najeriya a karo na biyu.

Da ya ke sanar da sakamakon zaben, Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban INEC, ya ce Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 15,191,847 da su ka bashi nasara a kan abokin hamayyar sa, Atiku Abubakar, na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 11,255,978.

Murnar samun nasara: Gwamoni da jiga-jigan 'yan APC sun ziyrarci Buhari, hotuna
Buhari yayin gaisawa da Ganduje
Asali: Twitter

Murnar samun nasara: Gwamoni da jiga-jigan 'yan APC sun ziyrarci Buhari, hotuna
Ganduje na magana da Buhari
Asali: Twitter

Murnar samun nasara: Gwamoni da jiga-jigan 'yan APC sun ziyrarci Buhari, hotuna
Buhari da Ganduje sun gaisa
Asali: Twitter

Murnar samun nasara: Gwamoni da jiga-jigan 'yan APC sun ziyrarci Buhari, hotuna
Gwamoni APC sun ziyrarci Buharia
Asali: Twitter

Farfesa Yakubu ya sanar da sakamakon zaben ne da misalin karfe 4:28 na safiyar yau, Laraba, bayan kammala karbar sakamakon zabe daga turawan zaben jihohin kasar nan 36 da birnin tarayya a daren jiya, Talata.

DUBA WANNAN: Ka yi koyi da Jonatahan – Jigo a PDP ya bawa Atiku shawara

Daga cikin gwamnonin da su ka ziyarci Buhari domin taya shi murnar akwai; Dakta Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, Barista Simon Lalong na jihar Filato, Umar Tanko Almakura na jihar Nasarawa da sauran su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel