Ina son zama kakakin Majalisar wakilan Najeriya – Gudaji Kazaure

Ina son zama kakakin Majalisar wakilan Najeriya – Gudaji Kazaure

Dan majalisar wakilai mai kuma babban dan kashenin shugaan kasa Muhammadu Buhari a majalisa, Honorabul Gudaji Kazaure ya ce babban burinsa bayan zabukan 2019 shi ne ya zama kakakin majalisar.

Honorabul Gudaji Kazaure ya sake lashe zaben mazabarsa ta Kazaure da Yankwashi da Roni da kuma Gwiwa a zaben yan majalisa da ya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

A wata hira da ya yi da BBC, Kazaure ya ce bai taba ganin zaben da ya burge shi wanda aka yi cikin tsari da kwanciyar hankali ba irin na bana.

Ina son zama kakakin Majalisar wakilan Najeriya – Gudaji Kazaure
Ina son zama kakakin Majalisar wakilan Najeriya – Gudaji Kazaure
Asali: Facebook

“Mutane sun fito sun zabi abin da suke so kuma sun nuna wa duniya cewa Najeriya kasa ce da ta san ‘yancin kanta, domin ‘yan Najeriya sun yarda da wakilcinmu shi ya sa suka kada wa jam’iyyarmu kuri’a,” in ji shi.

Kazaure ya ce bai kamata jam’iyyar adawa ta PDP ma ta dinga zargin an yi magudin zabe ba, don kuwa “kowa ya shaida an yi sahihin zabe.”

KU KARANTA KUMA: Nasarar lashe zabe: Kasar China ta taya Buhari murna

Ya kuma mika godiyarsa ga al’ummar mazabarsa tare da yi musu alkawarin cewa zai sake jajircewa wajen tabbatar da yi musu wakilci nagari.

Ya kuma bayyana aniyarsa na son takarar kujerar kakakin majalisar wakilai idan har Allah ya bashi dama.

Kazaure ya ce hakan ba zai zama wata matsala ba, sannan zai bai wa bangaren shugaban kasa damar cin kare ba babbaka, domin ya san duk abin da shugaban kasar zai aiki to, mai kyau ne.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel