Yadda APC tayi magudi a kasa kaf, don kayar da mu - Dr. Ardo na PDP

Yadda APC tayi magudi a kasa kaf, don kayar da mu - Dr. Ardo na PDP

- Wani shugaban PDP ya zargi cewa an tafka magudin zabe a zaben ranar asabar da ta gabata

- Yace sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta bada bashi da amfani

- Idan aka dubi yanayin magudin za a gane cewa akwai sarkakiya a lamarin

Yadda APC tayi magudi a kasa kaf, don kayar da mu - Dr. Ardo na PDP
Yadda APC tayi magudi a kasa kaf, don kayar da mu - Dr. Ardo na PDP
Asali: UGC

Wani shugaban jam'iyyar PDP Dr. Umar Ardo ya kwatanta sakamakon zaben asabar da ta gabata da sakamako mara amfani.

A wata takarda da Ardo yasa hannu, ya kwatanta sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta bada da sakamakon gyare gyare da juya sakamako na jam'iyyar APC.

Ya nuna cewa wadanda aka hada kansu don magudin sun bawa Buhari kuri'u masu yawa a inda suka san suna da magoya baya da yawa tare da rage kuri'u a yankunan da suke da adawa mai karfi.

Yadda APC tayi magudi a kasa kaf, don kayar da mu - Dr. Ardo na PDP
Yadda APC tayi magudi a kasa kaf, don kayar da mu - Dr. Ardo na PDP
Asali: Instagram

"Duk wanda ya damu har ya duba sakamakon, zai ga cewa akwai dabarbaru da aka shirya waken saka kuri'un idan aka danganta da sakamakon zaben da ya gabata,"

"Wannan lokacin ne suka rage kuri'u da PDP ke dasu a yankin kudu maso gabas da kudu kudu. Sunyi hakan ma a yankunan kirista dake arewa, amma sai suka bar tazara kadan."

GA WANNAN: An kama wata malama da laifin fyade ga wata yarinya a jihar Ikko

"Amma kuma a dabarance suka tsare yawan kuri'u a guraren da suke goyon bayan Buhari tare da tsare tazarar su da PDP. Duk anyi hakan ne don bawa Buhari kuri'u fiye da Atiku. Kowa zai iya gano wannan sarkakiyar," Ardo ya zarga.

Ardo ya nuna tabbacin shi na cewa kotu zata amince da amfani da fasahohin bincike wajen bayyana magudin zabe.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel