Ka yi koyi da Jonatahan – Jigo a PDP ya bawa Atiku shawara

Ka yi koyi da Jonatahan – Jigo a PDP ya bawa Atiku shawara

Prince Tony Momoh, tsohon minstan yada labarai, ya bawa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam’iiyyar PDP a zaben ranar Asabar, 23 ga watan Fabarairu, shawarar cewa ya rungumi kaddara, ya taya Buhari murnar lashe zabe.

Momoh ya bawa Atiku wannan shawara ne a yau, Laraba, yayin da ya ke Magana ta wayar tarho da kamfanin dillancin labarai na kasa (NANN) a kan sakamakon zaben shugaban kasa da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana.

Da ya ke sanar da sakamakon zaben, Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban INEC, y ace Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 15,191,847 da su ka bashi nasara a kan abokin hamayyar sa, Atiku Abubakar, na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 11,255,978.

A wani jawabi da ya fitar bayan shugaban INEC ya bayyana sakamako, Atiku y ace akwai alamun tambaya a kan sakamakon zaben tare da ikirarin cewar zai kalubalance shi a kotu.

Ka yi koyi da Jonatahan – Jigo a PDP ya bawa Atiku shawara
Atiku da Buhari
Asali: UGC

Momoh ya ce kimar Atiku za ta karu a gida Najeriya da kuma a idon duniya idan ya rungumi kaddara, ya karbi sakamakon zaben a matsayin zabin ‘yan Najeriya.

Tsohon ministan ya shawarci Atiku da kar ya tafi kotu tare da yin kira gare shi da ya dauki wayar sa ya kira Buhari, ya taya shi murna kamar yadda tsohon shugaban kasa Jonatahan ya yi a shekarar 2015 da Buhari ya kayar da shi zabe, lamarin da Momoh ya ce ya kara wa Jonathan kima a idon ‘yan Najeriya da ma duniya baki daya.

DUBA WANNAN: Ka rungumi kaddara kawai - Dele Momodu ya bawa Atiku shawara

Ina kira ga abokin mu, Atiku, da ya kira Buhari ya taya shi murna. Yin hakan zai saka shi zama gwarzo kamar yadda ta faru da tsohon shugaban kasa Jonatahan.

“Duk da yana da zabin zuwa kotu, amma zan shawarce shi da kar ya yi hakan domin ba zai samu karin mutunci a idon jama’a ba bayan kamala shari’a. Kar Atiku ya bari a yaudare shi, gara ya kira Buhari ya taya shi murna kawai,” a cewar Momoh.

Kazalika, Momoh ya bayyana cewar ya amince a kan cewar sakamakon zaben ya yi daidai da abin da jama’ar Najeriya su ka zaba, ya na mai nanata cewar rungumar kaddara ce kawai hanyar za ta kara wa Atiku kima da mutunci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel