Ahmed Musa ya taka rawar murnar nasarar shugaba Buhari (Bidiyo)

Ahmed Musa ya taka rawar murnar nasarar shugaba Buhari (Bidiyo)

Shahararren dan kwallon kafarnan na Najeriya, Ahmed Musa shima ya shiga sahun miliyoyin al’ummar duniya dake taya shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari murnar samun nasara a zaben shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar APC.

Ahmed Musa ya bayyana farin cikinsa da nasarar da shugaban kasa Buhari ya samu na zarcewa akan karagar mulki ne a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Instagram, inda ya rubuta “Ina taya shugabana Muhammadu Buhari murna.”

KU KARANTA: Yan Kaduna sun yaba ma INEC, sun bukaci Buhari ya kare martabar Najeriya

Ahmed Musa ya taka rawar murnar nasarar shugaba Buhari (Bidiyo)
Ahmed Musa da Buhari
Asali: UGC

Sai dai dan fitaccen dan wasan bai tsaya nan ba, inda ya daura bidiyonsa yana tikar wata sabuwar rawa da ake yayi a tsakanin matasan Najeriya, wanda ake yi ma lakabi da suna ‘Zanku’, ya cashe kwarai a cikin wannan bidiyo da yayi a dakin motsa jiki na kungiyar kwallon kafar da yake wasa.

A daren Laraba 27 ga watan Feburairu ne shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu ya sanar da Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a karo na biyu, inda ya samu kuri’u miliyan 15.19, yayin da Atiku Abubakar ya samu miliyan 11.26.

Ga bidiyon kamar yadda wani ma'abocin Facebook Magaji Ontop Daura ya daura shi.

Wannan sakamako ya nuna shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lallasa Atiku Abubakar ne da bambamcin kuri’u miliyan uku da dubu dari tara da ashrin da takwas, da dari takwas da sittin da tara (3,928,869).

Ahmed Musa ya sauya sheka daga kungiyar kwallon kafa Leicester City dake kasar Ingila inda ya koma kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr dake kasar Saudi Arabia, inda ya zamo dan wasan da yafi tsada a tarihin kungiyar.

Zuwa yanzu ya zura kwallaye biyar cikin wasanni goma sha biya, kuma ana sa ran Musa zai taka rawar gani a babban wasan da kungiyar zata kara da Al Shabab a ranar Alhamis, kamar yadda sa ran zai taka rawar gani a wasan abota tsakanin Najeriya da kasar Seychelles.

A wani labarin kuma, a kwanakin baya ne mahaifiyar dan wasan mai suna Sarah Moses ta rigamu gidan gaskiya bayan wata gajeruwar rashin lafiya, Saraha Moses yar asalin garin Kalaba na jahar Kros Ribas ta rasu ta bar Ahmed da yan uwansa mata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel