Nasarar lashe zabe: Kasar China ta taya Buhari murna

Nasarar lashe zabe: Kasar China ta taya Buhari murna

A ranar Laraba, 27 ga watan Fabrairu ne kasar China ta taya shugaan kasa Muhammadu Buhari murnar sake lashe zabe a matsayin shugaban kasar Najeriya a karo na biyu.

Lu Kang ya bayyana a taron manema labarai a Beijing cewa Najeriya ta kasance takwaran dabaru a ma’aikatar ta na kasashen Afrika.

“Kasar China ta dauki dangantakarta da Najeriya da muhimmanci sannan kuma a shirye take don yin aiki tare da sabuwar gwamnati don inganta harkar kasuwanci da hadin kai ta fannoni daban daban don samun amfani ga kasashen biyu,” A cewar Lu.

Nasarar lashe zabe: Kasar China ta taya Buhari murna
Nasarar lashe zabe: Kasar China ta taya Buhari murna
Asali: UGC

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta bayyana a safiyar Laraba cewa shugaban kasa mai ci kuma dan takaran Shugaban kasa a jam’iyyar All Progressives Congress, ya lashe zabe da kashi 55 na ingantattun kuri’u a zaben shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Buhari bai yi umurnin cewa a harbi yan Najeriya saboda satar akwatunan zabe ba – Tinubu

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Bayan da aka fadi sakamakon zaben Najeriya, hannayen jari kan kudin Naira da Najeriya ke sayarwa a kasar sun daga da kashi kusan goma cikin dari.

An yi zaben ne a ranar asabar da ta gabata, wanda ya zo ya wuce lami lafiya ba tare da manyan tashe-tashen hankula ba.

Yawancin hannayen jari suna zubewa ne sakamakon rashin tabbas da ma tsoron wanda ya zama shugaba a kasashen duniya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel