2019: Shugaba Buhari ya karbi satifiket din nasara a hannun INEC

2019: Shugaba Buhari ya karbi satifiket din nasara a hannun INEC

- INEC ta tabbatar da Buhari a matsayin wanda ya ci zaben 2019

- Hukumar zaben ta mikawa Shugaba Buhari satifiket din nasara

- Buhari yayi jawabi bayan ya karbi takardar shaidar lashe zaben

Hukumar zabe mai zaman kan-ta a Najeriya watau INEC, ta mikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma Abokin takarar sa, Yemi Osinbajo, takardar shaida na lashe zaben shugaban kasa da aka yi kwanan nan a Najeriya.

INEC ta ba shugaban kasar mai-ci satifiket din da ke nuna cewa shi ya zo na farko a zaben da aka yi a karshen makon da ya gabata. Shugaban kasar ya godewa duk wadanda su ka zabe sa a jawabin da yayi a gaban jama’a a Garin Abuja.

KU KARANTA: APC tana zargin Gwamnan ta game da rashin nasarar Buhari a Jihar sa

Kamar yadda mu ka samu labari, shugaban kasar ya kuma nuna jimamin sag a wadanda su ka rasa iyalan su da ‘yan uwa a dalilin rikicin da ya barke lokacin zabe. An rahoto cewa an samu hatsaniya a dalilin babban zaben da aka yi.

Shugaba Muhammadu Buhari yayi jawabi dazu a wajen taron majalisar APC inda ya jinjinawa duk wadanda su ka taimaka wajen ganin ya sake zarcewa a kan mulki. Buhari ya doke Alhaji Atiku Abubakar ne da kuri’a 15, 191, 847.

Dazu kun ji labari cewa kasashen Afrika su na farin ciki da nasarar da Buhari ya samu a zaben na bana. Shugaban kasar Senagal, Ghana, Zimbabwe, Nijar duk sun aiko sako su na taya Buhari murnar doke PDP.

Buhari a kan hanyar sa ta karbar shaidar cin zabe

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel