Kasashen Senagal, Ghana, Zimbabwe, Nijar sun taya Buhari murnar doke Atiku

Kasashen Senagal, Ghana, Zimbabwe, Nijar sun taya Buhari murnar doke Atiku

Mun ji labari cewa shugabannin kasashen Nahiyar Afrika irin su Sanagal, Ghana, Zimbabwe, da makwabta Nijar sun aiko da sakon taya murnar su ga shugaba Buhari na samun nasara a zaben 2019.

Kasashen Senagal, Ghana, Zimbabwe, Nijar sun taya Buhari murnar doke Atiku
Kasashen Afrika su na farin ciki da nasarar da Buhari ya samu
Asali: Facebook

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai watau Femi Adesina ya bayyana cewa shugabannin Afrika na kasashe 3 sun aika sakon taya murnar su ga shugaba Muhammadu Buhari a sakamakon tazarce da aka zabe sa yayi.

Femi Adesina yace Nana Koffi-Addo na kasar Ghana, da kuma shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyyar Nijar sun aikowa Muhammadu Buhari sako na musamman su na taya sa murnar lashe zaben shugaban kasa da aka yi a Najeriya.

KU KARANTA: ‘Dan takarar Jam’iyyar PDP yace an murde zaben Shugaban kasa

Mai magana da yawun bakin shugaban na Najeriya ya kuma bayyana cewa shugaba Macky Sall na kasar Sanagal ya taya shugaba Buhari murnar sake samun damar ya cigaba da jan ragamar shugabancin Najeriya na wasu shekaru 4.

Yanzu nan ne kuma mu ke jin cewa gwamnatin kasar Zimbabwe ta Gabashin Afrika ta aiko na ta sakon taya murnar. Shugaban na Zimbabwe ba a bar sa baya ba, inda yayi wa Buhari addu’a ya iya sauke nauyin da mutanen kasar su ka daura masa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel