Da duminsa: Atiku zai gabatar da jawabi ga duniya yau

Da duminsa: Atiku zai gabatar da jawabi ga duniya yau

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, zai gabatar da da jawabi ga duniyar yan jarida a ranan LAraba, 27 ga watan Febrairu, 2019 a babbar birnin tarayya Abuja.

Atiku wanda yayi takarar kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP ya fadi a zaben shugaban kasa da aka gudanar zaiyi magana ka zaben.

Bisa ga cewa Sakataren shirye-shiryen PDP, Austin Akobundu, za'a yi taron ne misalin karfe 4 na yamma a farfajiya Umaru Musa Yar'adua Center.

Mun kawo muku rahoton cewa dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce ba zai aminta ba da sakamakon babban zaben kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu 2019. Ya ce zaben cike yake da murdiya gami da rashin gaskiya.

Atiku Abubakar, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyar PDP, ya ce ba zai taba amincewa da sakamakon babban zaben kasa da hukumar INEC ta bayyana a yau Laraba, 27 ga watan Fabrairun 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel