Zahra Buhari-Indimi ta saki zafafan hotuna domin bikin zarcewar mahaifinta

Zahra Buhari-Indimi ta saki zafafan hotuna domin bikin zarcewar mahaifinta

A ranar Laraba, 27 ga watan Fabrairu ne dai aka kaddamar da Shugaban kasa Muhammdu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben Shugaban kasa na 2019. Yan Najeriya ne dai suka zabi Shugaban kasar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

Bayan an kaddamar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben, yar Shugaban kasa Buhari, Zahra Buhari-Indimi ta je shafin zumunta domin taya mahaifinta murna.

A wani hoto da Zahra ta wallafa a shafinta na Instagram, an gano Shugaban kasar tare da yarsa da kuma surukinsa, Ahmed Indimi.

An gano su uku suna murmushi mai kayatarwa a hoton bayan nasarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

KU KARANTA KUMA: Yan Najeriya sun caccaki babban faston da yayi ikirarin cewa Buhari ba zai zarce ba (bidiyo)

A rubutun da ta wallafa jikin hoton ta roki Allah da ya kare Najeriya daga mugun nufi.

Ta rubuta "May Allah liberate Nigeria from all evil. Ameen ya rabbi. Ya Allah ba dan halinmu ba Ya Allah ka kiyaye mana fitintinu ka daukaka kasan mu Ameen. ❤️"

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel