Yan Kaduna sun yaba ma INEC, sun bukaci Buhari ya kare martabar Najeriya

Yan Kaduna sun yaba ma INEC, sun bukaci Buhari ya kare martabar Najeriya

Tun bayan da shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu ya sanar da Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa ne aka shiga halin farin ciki da annushuwa a tsakanin al’umma mazauna jahar Kaduna.

A daren Laraba 27 ga watan Feburairu ne shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu ya sanar da Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a karo na biyu, inda ya samu kuri’u miliyan 15.19, yayin da Atiku Abubakar ya samu miliyan 11.26.

KU KARANTA: Nasara: Banda cin mutuncin abokan hamayya – Buhari ga magoya bayansa

Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito jama’an jahar sun yi kira da babban murya ga shugaban kasa Buhari da ya tabbata ya sanya Najeriya a gabansa fiye da duk wasu bukatunsa, don haka suka nemi Buhari ya zage damtse wajen kare martabar Najeriya.

Wani mazaunin Kaduna, Muhammad Auwal da majiyarmu ta tattauna dashi ya bayyana jin dadinsa da nasarar da Buhari ya samu, sa’annan yayi kira a gareshi daya kasance mai rikon amana game da nauyin da aka daura masa.

Haka zalika shima wani mutumi mai suna Sani Haruna yayi kira ga shugaba Buhari daya ji tsoron Allah ya kula da dimbin talakawan da suka fito suka zabeshi, kada ya manta dasu, don haka ya nemi daya mayar da hankali game da gyaran sha’anin ilimi da kuma samar da aikin yi.

Yayin da wasu ke yin kiraye kiraye ga shugaba Buhari, wasu mazauna jahar kuma sun jinjina ma hukumar zabe mai zaman kanta INEC, bisa kokarin da tayi wajen shiryawa tare da gudanar da ingantaccen zabe mai tsafta, inda suka bayyana zaben a matsayin daya daga cikin zabukan adalci da aka taba yi a Najeriya.

Malam Usman Musa ya shaida ma majiyarmu cewa “Anyi zabe lafiya, sai dai an samu wasu yan tashin tashina a wasu sassan jahar, amma dai kasan ba’a raba zabe da ireiren wannan rikie rikice. Ina kira ga Atiku daya rungumi kaddara.”

Shima wani mai suna Usman Sani cewa yayi “Mun yi addu’ar Allah Ya zaba mana shugaba nagari, kuma Ya zaba mana Buhari, muna fatan Buhari zai cigaba da shugabanci nagari a Najeriya.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel