Ana maidawa juna kalamai tsakanin manyan APC bayan Atiku ya kawo Adamawa

Ana maidawa juna kalamai tsakanin manyan APC bayan Atiku ya kawo Adamawa

Mun ji wasu manyan ‘yan siyasa da ke karkashin tafiyar jam’iyyar APC mai mulki da ke jihar Adamawa da kuma Garin Abuja su na zargin juna game da nasarar da PDP ta samu a jihar a zaben da aka yi.

Ana maidawa juna kalamai tsakanin manyan APC bayan Atiku ya kawo Adamawa
APC ta fadi dalilin da ya sa Atiku ya ci zaben Adamawa
Asali: Facebook

Kamar yadda labari ya zo mana, ana samun rikici tsakanin manyan APC bayan da jam’iyyar ta rasa kujerar Sanata har 2 a Adamawa, sannan kuma jam’iyyar mai mulki ta rasa kujeru har 4 cikin 8 da ake su da ‘yan majalisar tarayya.

Ambasada Aminu Iyawa ya fitar da jawabi jiya Talata a Garin Yola a madadin kusoshin APC na jihar inda yace jam’iyyar ta su ta sha kashi ne saboda gwamna Jirbila Bindow. Iyawa yace gwamna Bindow ne yake yi wa APC zagon kasa.

Aminu Iyawa yake cewa tun tuni su ka nuna shakkun su game da nasarar shugaba Buhari a jihar Adamawa, amma yace wasu ‘yan APC su kayi da su har jama'a su na sukar su da sunan cewa su na yi wa gwamnan jihar adawa.

KU KARANTA: Abin da ya sa Saraki ya sha kasa wannan karo – Inji wani Sanatan APC

Shi ma dai Dr Mahmood Halilu wanda ‘Dan uwa ne a wajen Uwargidar shugaban kasa, ya bayyana cewa babu wanda za a ga laifin sa wajen rashin nasarar da APC ta samu a Adamawa sai gwamna. Halilu yace hakan bai ba su mamaki ba.

Kwamishinan yada labarai na Adamawa, Malam Ahmad Sajoh, yayi tir da kalaman da wadannan manyan jam’iyya su ke fada. Ahmad Sajoh masu wadannan magana su ne ainihin wadanda su ka yi wa APC zagon kasa a Adamawa a zaben.

Kwamishin nan jihar yana zargin wadannan ‘yan APC da jefa jam’iyyar cikin rami a zaben shugaban kasar da aka yi domin kurum mutane su ga bakin jinin gwamna. Shi ma wani jami'in APC a Adamawa ya tabbatar mana da wannan zargi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel