Hannayen jarin Najeriya a kasuwannin duniya ta daga, bayan Buhari yayi nasara

Hannayen jarin Najeriya a kasuwannin duniya ta daga, bayan Buhari yayi nasara

- Hannayen jari kan kudin Naira da Najeriya ke sayarwa a kasar sun daga da kashi kusan goma cikin dari

- Hakan ya biyo bayan fadin sakamakon wanda ya lashe zaben shugaban kasa da ya gudana a ranar Asabar da ya gabata

- Yawancin hannayen jari suna zubewa ne sakamakon rashin tabbas da ma tsoron wanda ya zama shugaba a kasashen duniya

Bayan da aka fadi sakamakon zaben Najeriya, hannayen jari kan kudin Naira da Najeriya ke sayarwa a kasar sun daga da kashi kusan goma cikin dari.

An yi zaben ne a ranar asabar da ta gabata, wanda ya zo ya wuce lami lafiya ba tare da manyan tashe-tashen hankula ba.

Yawancin hannayen jari suna zubewa ne sakamakon rashin tabbas da ma tsoron wanda ya zama shugaba a kasashen duniya.

Hannayen jarin Najeriya a kasuwannin duniya ta daga, bayan Buhari yayi nasara
Hannayen jarin Najeriya a kasuwannin duniya ta daga, bayan Buhari yayi nasara
Asali: UGC

Shi dai wannan hannun jari, da Najeriya ke sayarwa wani kudi ne da ake sayarwa kamar bashi, in aka saya Sai ya sami kudin kashewa.

KU KARANTA KUMA: Nasarar zabe: Yan Igbo sun taya Shugaban kasa Buhari murna

Shi kuma wanda ya saya, sai ya sayar bayan wasu shekaru in sun Kara riba a kai ko kudin ruwa.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Yan Najeriya sun caccaki wani malamin addini mai suna Prophet Samuel Akinbodunse ayan yayi ikirarin cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai lashe zabe ba a karo na biyu.

Faston yayi ikirarin cewa an kadarta wa Buhari shugabanci sau guda yana kacal. A cikin wani shahararren bidiyo, faston yayi ikirarin cewa Shugaban kasar zai rasa ransa idan ya nemi zarcewa saboda sau daya aka kadarta mai mulkin kasar.

Akinbodunse yayi ikirarin cewa Shugaban kasar zai mutu kafin yan Najeriya su kai ga zabar wanda zai zamo Shugaban kasarsu na gaba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel