Kotun duniya ta ICC zamu kai manyan sojin da suka zo yiwa Buhari magudi a jiharmu - Wike

Kotun duniya ta ICC zamu kai manyan sojin da suka zo yiwa Buhari magudi a jiharmu - Wike

- Gwamnan jihar Rivers ya neme ICC data gurfanar da GOC na division 6 na sojin Najeriya

- Gwamnan yace GOC ya dauki rayukan al'ummar jihar Rivers a hannun sa

- Zai bayyanawa yan Najeriya dalilin daya sanya division 6 tattara bayanan zaben wasu kananan hukumomin jihar

A gaskiya PDP na sanya ma'aikatanmu cikin hadari - INEC ta koka
A gaskiya PDP na sanya ma'aikatanmu cikin hadari - INEC ta koka
Asali: Depositphotos

Gwamna jihar Rivers Mr Nyesom Wike yace gwamnatin jihar sa ta nemi ICC data tuhumi general officer commanding (GOC) division 6 na sojin Najeriya Major General Jamil Sarhem.

Wike yace a maimakon kwana- kwana GOC ya fito ya bayyanawa yan Najeriya dalilin daya sanya division 6 afkawa jami'an hukumar zabe a Ikwerre,Emohua da Okrika wanda ake zargin satar kayan zabe ne da shirin fitar da sakamako.

GA WANNAN: Majalisar dattijai ta dawo, ko dattijo Saraki ya sami halarta?

Gwamnan ya kara da cewa GOC ya dauki rayukan al'ummar jihar Rivers da hannun sa inda yace duk wani bayani nashi da bashi da tabbas bazai sanya a fasa gurfanar dashi ba.

Gwamnan ya kara da cewa suna iyakar kokarin su tare da ICC kuma zasu nemawa wadanda sojin suka kashe su a wajen zaben adalci.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel