Yan Najeriya sun caccaki babban faston da yayi ikirarin cewa Buhari ba zai zarce ba (bidiyo)

Yan Najeriya sun caccaki babban faston da yayi ikirarin cewa Buhari ba zai zarce ba (bidiyo)

Yan Najeriya sun caccaki wani malamin addini mai suna Prophet Samuel Akinbodunse ayan yayi ikirarin cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai lashe zabe ba a karo na biyu. Faston yayi ikirarin cewa an kadarta wa Buhari shugabanci sau guda yana kacal.

A cikin wani shahararren bidiyo, faston yayi ikirarin cewa Shugaban kasar zai rasa ransa idan ya nemi zarcewa saboda sau daya aka kadarta mai mulkin kasar.

Akinbodunse yayi ikirarin cewa Shugaban kasar zai mutu kafin yan Najeriya su kai ga zabar wanda zai zamo Shugaban kasarsu na gaba.

Faston harma yayi kira ga mambobin cocinsa da suyi Magana da Shugaban kasar domin ya saurari shawararsa sannan kada yayi kamfen din neman zarcewa.

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar PDP ta ki amincewa da sakamakon zabe

Sai dai kuma cikin nasara Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi kuri’u sannan kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kaddamar da shi a matsayin Shugaban kasa 2019.

Hakan yasa yan Najeriya da dama suka caccaki faston akan ikirarin karyar da yayi. Da dama sun je shafin Facebook inda ya wallafa bidiyon da yake ikirarin sannan suka caccaki a zauren nuna ra’ayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel