Kotu ta kori kara kan wai rashin takardun makarantar shugaba Buhari

Kotu ta kori kara kan wai rashin takardun makarantar shugaba Buhari

- Wata babbar kotun dake Fatakwal tayi wats da karar shugaban kasa da aka kai

- Ana bukatar ya bayyana takardar shaidar makarantar shi ga kotun da kuma hukumar zabe mai zaman kanta

- Alkalin yayi watsi da karar ne ganin cewa bata da wani amfani

Kotu ta kori kara kan wai rashin takardun makarantar shugaba Buhari
Kotu ta kori kara kan wai rashin takardun makarantar shugaba Buhari
Asali: Instagram

Wata babban kotu dake a Fatakwal, jihar Rivers ta kori karar da aka kai don hana shugaban kasa Muhammadu Buhari takara 2019 sakamakon rashin takardun makarantar shi.

Wani Lauya Lezina Amegua, ya roki kotu da tasa hukumar zabe da ta hana shugaban kasar takara. Amma mai shari'a Ishaq Sani, ya kori shari'ar sakamakon rashin amfani. Mai shari'ar yace shi bai ga yanda bayyana takardar shaidar makaranta ko madadin fa ya shafi ra'ayin shi ba a matsayin dan takara.

GA WANNAN: An kama wata malama da laifin fyade ga wata yarinya a jihar Ikko

Kotun tace bazata lamunta ayi amfani da ita ba ga yan bata suna, azarbabi da shishigi wadanda basu san kan abinda ma suke kara ba.

A karar harda jam'iyyar APC da kuma Attorney- General din kasar.

Amegua ya bukaci kotun ta ba wa shugaban kasar umarnin ya bayyana takardar shaidar makarantar shi ga kotu da kuma hukumar zabe mai zaman kanta.

Shugaban yayi watsi da karar sakamakon karar bata da wani amfani.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel