Nasarar zabe: Yan Igbo sun taya Shugaban kasa Buhari murna

Nasarar zabe: Yan Igbo sun taya Shugaban kasa Buhari murna

Kungiyar yan Igbo mai suna Ndigbo Unity Forum (NUF), sun taya Shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar sake cin zabe a karo na biyu.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta kaddamar da Shugaban kasa Buhari na jam’iyyar the All Progressives Congress (APC) a matsayin wanda ya lashe zabe bayan ya samu kurí’u 15,191,847 sannan ya kawo jihohi 19.

Buhari ya kayar da sauran yan takara 72 ciki harda Atiku Abubakar wanda ya samu kuri’u 11, 255,978 sannan ya kawo jihohi 17 harda birnin tarayya.

Shugaban kungiyar NUF, Mista Augustine Chukwudum, ya mika sakon taya murnar ne a wata hira da NAN a Enugu inda ya bukaci yan Najeriya da su ci gaba da kwantar da hankulansu.

Chukwudum ya bayyana cewa ya zama dole a yaba ma yan Najeriya da suka fito kwansu da kwarkwata domin zabar Shugaban kasarsu.

Ya shawarci duk jam’iyyar da bata aminta da sakamakon ba da ta shigar da kara kotu.

KU KARANTA KUMA: Zaben Shugaban kasa: Ku kwantar da hankalinku – PDP ga yan Najeriya

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Laraba, 27 ga watan Fabrairu ta ki rattaba hannu a takardan sakamakon zabe wanda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) dake Abuja ta gabatar.

Hukumar INEC ta bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wanda yayi nasaran samun kuri’u 15,191,847 inda ya doke abokin adawarsa, Atiku Abubakar wanda ya samu kuri’u 11262,987.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel