Zaben Buhari: Ganduje ya jinjinawa Kanawa

Zaben Buhari: Ganduje ya jinjinawa Kanawa

A yau Laraba ne gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi jinjina ga al'ummar jihar Kano saboda bawa Shugaba Muhammadu Buhari kuri'u mafi tsoka a zaben 2019.

Shugaba Buhari ya samu kuri'u 1,464,768 daga jihar Kano wanda hakan ya yi dai-dai da kashi 78.9 cikin dari na kuri'un jihar a zaben shugaban kasa da aka kammala.

A jawabin da ya yi a wurin taron masu ruwa da tsaki a jihar Kano bisa nasarar da Buhari ya samu, gwamnan ya ce kuri'un da Kanawa suka bawa Buhari ya nuna sun amince da tsare-tsaren gwamnatin Buhari.

DUBA WANNAN: Yadda Buhari ya yi murdiyya wajen lashe zaben 2019 - Sheikh Ahmad Gumi

Ganduje ya jinjina wa Kanawa saboda bawa Buhari kuri'u mafi yawa
Ganduje ya jinjina wa Kanawa saboda bawa Buhari kuri'u mafi yawa
Asali: Depositphotos

Ya ce: "Ya dace mu mika godiyar mu ga al'ummar jihar Kano saboda yadda suka fito kwansu da kwarkwata suka bawa shugaba Muhammadu Buhari kuri'u mafi yawa a zaben shugaban kasa da aka kammala."

Ya yayin da ya ke yabon al'ummar, Gwamna Ganduje ya kuma bukaci al'umma su fito kwansu da kwarkwata a lokacin zaben gwamnonin jiha da 'yan majalisar jiha, "saboda su fara more romon demokradiyya a dukkan lunguna da sakuna na jihar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel