‘Yan Sandan Najeriya sun bada belin Farfesa Maurice Iwu

‘Yan Sandan Najeriya sun bada belin Farfesa Maurice Iwu

Mun samu labari cewa jami’an ‘yan sandan Najeriya sun saki tsohon shugaban INEC na kasa, Farfesa Maurice Iwu wanda aka damke kwanan nan. A jiya ne aka bada belin Farfesan a babban birnin jihar Imo.

‘Yan Sandan Najeriya sun bada belin Farfesa Maurice Iwu
Magu ya kama wanda ya taba shirya zaben a Najeriya
Asali: Getty Images

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Imo, CP Dasuki Galadanchi, ya bayyanwa Duniya cewa sun bada belin Maurice Iwu bayan ya shiga hannun su. A cikin ‘yan kwanakin nan ne jami’an ECC su ka sa a ka kawo masu tsohon shugaban INEC.

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa ta kama Maurice Iwu ne bayan ta samu izni daga hannun ‘yan sanda. Wannan ya sa jami’an tsaro na Imo su ka kira Farfesan ya kawo kan sa har gaban su da kan sa.

KU KARANTA: Sheikh Gumi ya koka da yadda jam'iyyar APC ta lashe zaben 2019

Kwamishinan na ‘yan sanda, bai bayyanawa ‘yan jarida abin da ya sa aka tsare Maurice Iwu ba. EFCC dai ta rubutawa rundunar ‘yan sandan da ke Garin Owerri takarda ne a lokacin da ake zabe cewa tana neman tsohon shugaban na INEC.

CP Dasuki Galadanchi yace yanzu an bada belin Farfesa Iwu saboda ganin mutuncin sa da shekarun sa da kuma la’akari da irin gudumuwar da ya ba a Najeriya a matsayin wanda ya jagorancin zaben shugaban kasa da aka yi a 2007.

Tuni dai Maurice Iwu ya rubuta jawabi a gaban ‘yan sanda bayan jami’an EFCC din sun taso sa a gaba tun daga garin Legas. Tsohon shugaban na INEC zai mika kan sa gaban EFCC nan gaba idan aka neme sa inji kwamishinan ‘yan sandan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel