Jam’iyyar PDP ta ki amincewa da sakamakon zabe

Jam’iyyar PDP ta ki amincewa da sakamakon zabe

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Laraba, 27 ga watan Fabrairu ta ki rattaba hannu a takardan sakamakon zabe wanda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) dake Abuja ta gabatar.

Hukumar INEC ta bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wanda yayi nasaran samun kuri’u 15,191,847 inda ya doke abokin adawarsa, Atiku Abubakar wanda ya samu kuri’u 11262,987.

Buhari yayi nasara a jihohi 19 sannan Atiku ya lashe jihohi 17 da Babban Birnin Tarayya.

Jami’in PDP, Mista Osita Chidoka, ya fita daga dakin gabatar da sakamakon zabe a lokacin da shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya nemi jami’an da su sa hannu a takardan sakamako.

Jam’iyyar PDP ta ki amincewa da sakamakon zabe
Jam’iyyar PDP ta ki amincewa da sakamakon zabe
Asali: Facebook

Chidoka, wanda ya kasance tsohon ministan jiragen sama, a hira da yayi da manema labarai a hanyar shi na zuwa waje, yace jam’iyyar bata amince ba da sakamakon zaben bisa dalilai uku da ta kawo a baya.

Ya bayyana cewa jam’iyyar ta kayautata zatton cewa hukumar INEC tayi amfani da na’urar card reader ne wajen kimanta sakamakon zaben.

KU KARANTA KUMA: Zaben Shugaban kasa: Ku kwantar da hankalinku – PDP ga yan Najeriya

Har ika yau dai, Chidoka ya kara da cewa jam’iyyar PDP tana a matsayinta na jam’iyya maikiyayewa: “mun yarda da doka, mun kuma yarda da kundin tsarin Najeriya.

Chidoka a baya yace sun nuna damuwa akan rashin amfani da na’urar card reader a zabe a wassu wurare kuma yayi kira ga hukumar INEC da ta gabatar da bayanai akan yawan masu zabe da aka tantance da na’urar card reader.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel