Zaben Shugaban kasa: Ku kwantar da hankalinku – PDP ga yan Najeriya

Zaben Shugaban kasa: Ku kwantar da hankalinku – PDP ga yan Najeriya

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ta bukaci yan Najeriya da su ci gaba da kwantar da hankalinsu yayinda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta kaddmar da Shugaban kasa Muhammadu Buari na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wanda ya lashe zaben ranar Asabar.

An kaddamar da Buhari a matsayin wanda yayi nasara bayan ya samu kuri’u 15,191,847 da kuma lashe jihohi 19 yayinda Peoples Democratic Party (PDP) kuma ta samu kuri’u 11, 255,978 sannan ta lashe jihohi 17 harda birnin tarayya, inda ta zamo na biyu.

Jami’in PDP kuma tsohon ministan sufuri, Osita Chidoka wanda yayi Magana bayan sanar da sakamakon karshe ya bukaci yan Najeriya da su kwantar da hankalinsu inda ya kara da cewa PDP ta yi imani da kundin tsarin mulkin Najeriya kuma tana nan akan tafarkin damokradiya.

Zaben Shugaban kasa: Ku kwantar da hankalinku – PDP ga yan Najeriya
Zaben Shugaban kasa: Ku kwantar da hankalinku – PDP ga yan Najeriya
Asali: Facebook

Da farko ya bukaci Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu da kada ya kaddamar da Buhari a matsayin Shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: Zaben Shugaban kasa: Ana bikin murnar nasarar Buhari a Maiduguri

Ya bayyana cea akwai masu zabe miliyan 5.1 da basu samu dammar jefa kuri’unsu ba sakamakon soke kuri’un, da sauransu. Ya bayyana cewa ba za’a iya watsi dasu ba saboda sun fi kuri’u miliyan 3.9 da Buhari ya dara babban abokin adawarsa, Atiku.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel