Hukumar INEC ta hana Mutanen Kasar Ibo yin zabe – Peter Obi

Hukumar INEC ta hana Mutanen Kasar Ibo yin zabe – Peter Obi

‘Dan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben da aka yi a karkashin jam’iyyar PDP, Peter Obi, ya koka game da zaben na 2019. Peter Obi yace hukumar INEC ta hana wasu mutanen kasar yin zabe.

Hukumar INEC ta hana Mutanen Kasar Ibo yin zabe – Peter Obi
Peter Obi ya zargi Hukumar INEC da hana mutanen sa yin zabe
Asali: UGC

Kamar yadda mu ka ji labari, Peter Obi, ya zargi hukumar zabe na INEC da kin ba jama’an da ke kudu maso gabas damar kada kuri’an su a zaben bana. Obi yace kashi 20% na Ibo ne kurum su ka iya yin zabe a shekarar nan.

Peter Obi ya bayyanawa ‘yan jarida cewa INEC ta kitsa yadda tayi wajen ganin mutanen da ke Kudu ta gabas ba su iya yin zabe ba. ‘Dan takarar ya kuma ce akwai alamar tambaya game da zaben da aka yi a Yobe da Borno.

KU KARANTA: APC ta nemi ayi watsi da zaben Shugaban kasa a Akwa Ibom

Obi yana mamakin irin tarin kuri’un da su ka fito daga jihohin na Arewa ta gabas inda ake fama da rikicin Boko Haram. Sannan kuma abokin ‘dan takarar na Atiku ya koka game da yadda na’urorin INEC da aka ce sun kone.

‘Dan takarar yace akwai kishin-kishin din magudi a yadda na’urori kusan 400, 000 da ake amfani da su wajen tantance masu kada kuri’a su ka kone kurmus. Wannan ta sa aka rika amfani ba tare da na’urorin ba a wasu wurare.

Wani bidiyo dai ya fito inda ake zargin cewa an tafka magudi a yankin Borno da Yobe inda APC ta sam gagarumar nasara. Kuri’un yankin duk da ana rikici, ya fi karfin abin da aka samu a irin su Anambra da Enugu inji Obi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel