Ana kishin-kishin din PDP za ta kalubalanci nasarar Buhari a kotu

Ana kishin-kishin din PDP za ta kalubalanci nasarar Buhari a kotu

Mun ji labari cewa ana tunani ‘dan takarar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ba zai amince da sakamakon zaben da aka yi a Najeriya ba. Jaridar The Cable ta kasar nan ta bayyana mana wannan.

Ana kishin-kishin din PDP za ta kalubalanci nasarar Buhari a kotu
'Dan takara PDP Atiku bai amince da nasarar Buhari a zaben 2019 ba
Asali: Facebook

Kamar yadda mu ke samun labari, Atiku Abubakar ya fara shirin tara manyan Lauyoyi da za su tsaya masa a kotu inda zai kalubalanci sakamakon zaben bana. PDP dai har yanzu ba tayi na’am da sakamakon zaben shugaban kasar ba.

Daga cikin Lauyoyin da ake tunani Atiku Abubakar zai yi hayar su akwai tsohon Ministan shari’a na Najeriya, Kanu Agabi. Haka kuma watakila ‘dan takarar na PDP ya tanadi Lauyoyi irin su Joe Gadzama da Chris Uche domin zuwa kotu.

KU KARANTA: 2019: Sakamakon zaben Jihar Sokoto ya ba jama'a mamaki

Ana shirin kammala tattara sakamakon zaben ne jam’iyyar PDP ta kira wani zaman a gaggawa wanda Sarkin yakin neman zaben Atiku Abubakar a zaben na 2019 watau Bukola Saraki ya jagoranta a wani dakin taro a Garin Abuja jiya Talata.

Jam’iyyar PDP dai ta nuna an yi coge a zaben inda ta nemi hukumar INEC ta dakatar da tattara sakamakon kuri’un domin kuwa akwai zaben jihohin da ba ta yarda da su ba. A zaben 2015, Goodluck Jonathan bai kai kara zuwa kotu ba.

A wancan zabe da aka yi lokacin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya kira Muhammadu Buhari wanda yayi nasara a wayar salula domin taya sa murna. Har yanzu dai Atiku bai kira Buhari ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel