Zaben Shugaban kasa: Ana bikin murnar nasarar Buhari a Maiduguri

Zaben Shugaban kasa: Ana bikin murnar nasarar Buhari a Maiduguri

Dubban matasa da ke murna sun fita unguwannin Maiduguri, babbar birnin jihar orno domin nuna farin ciki akan nasarar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu a zaben Shugaban kasa da ya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa matasan a ranar Laraba, 27 ga watan Fabrairu sun yi wasti da dokar ta baci da ke yankin inda suka yi tururuwar fitowa a unguwanni suna kada ganga da wake-waken jam’iyyar domin bikin nasarar Shugaban kasar.

Zaben Shugaban kasa: Ana bikin murna a Maiduguri kan nasarar Buhari
Zaben Shugaban kasa: Ana bikin murna a Maiduguri kan nasarar Buhari
Asali: Twitter

Matasan sun bayyana cewa sun kalli sakamakon zaben wanda Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu cewa suna jin cewa an sanar da sakamakon da karfe 4.37 a.m na ranar Laraba sai kawai burinsu ya cika.

KU KARANTA KUMA: Cikakken jawabin da Buhari ya yi bayan INEC ta sanar da nasarar daya samu

Shugaban INEC ya kaddamar da sake zabar Buhari, bayan ya ssamu kuri’u 15,191,847, inda yayi nasara a jihohi 19 yayinda ya kayar da sauran yan takara 72, ciki harda Atiku Abubakar dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) wanda ya samu kuri’u 11,255,978 sannan ya lashe jihohi 17 harda birnin tarayya.

Wasu mazauna Maiduguri da ke farin ciki sun bayyana cewa tazarcen Buhari nasara ce ga yan Najeriya da damokradiyya. Cewa hakan ya nuna shine muradin yan Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel