Son-kan Bukola Saraki ne ya sababin faduwar sa zabe – Abu Ibrahim

Son-kan Bukola Saraki ne ya sababin faduwar sa zabe – Abu Ibrahim

Mun ji cewa wani babban ‘dan majalisar dattawan Najeriya, Sanata Abu Ibrahim, yayi magana game da rashin nasarar da shugaban majalisar tarayya, Bukola Saraki, ya samu a zaben 2019 da aka yi.

Son-kan Bukola Saraki ne ya sababin faduwar sa zabe – Abu Ibrahim
Dama mun yi alkawarin yi wa Saraki ritaya a 2019 – Sanatan Katsina
Asali: Facebook

Sanatan jam’iyyar APC na Yankin Katsina, Abu Ibrahim yana ganin cewa son kai irin na Bukola Saraki ne ya jawo masa faduwa zaben bana. ‘Dan majalisar yace Bukola Saraki mutum ne wanda bai san kowa ba sai karon kan sa.

Abu Ibrahim ya bayyana wannan ne lokacin da ya gana da manema labarai a Abuja Ranar Talata. Ibrahim yace mutanen Kwara sun ki zaben Sanata Bukola Saraki ne saboda irin kwadayin sa da rashin taimakawa mutanen sa.

KU KARANTA: Yarinyar Sanata Mark ta doke Jam’iyyar Mahaifin ta a zaben 2019

Shugaban kwamitin na kwadago a majalisar dattawan kasar yace al’ummar Kwara ta tsakiya inda shugaban majalisar dattawan ya fito, sun yi hankali a wannan karo, don haka su kayi waje da shi da sauran ‘yan majalisun PDP.

‘Dan majalisar na yankin Kudancin jihar Katsina ya bayyana cewa APC ta sha alwashin yi wa Saraki ritaya a zaben nan, kuma haka aka yi. Sanatan yace sun shiga lungu-lungu na Kwara inda su ka gane Saraki bai da farin jini.

Babban Sanatan dai ba zai nemi wata kujera ba wannan karo, sai dai yana sa rai cewa majalisar nan ta bana ta fi wanda Bukola Saraki ya jagoranta a baya saboda tsofaffin hanu da ake samu a APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel