Nasara: Banda cin mutuncin abokan hamayya – Buhari ga magoya bayansa

Nasara: Banda cin mutuncin abokan hamayya – Buhari ga magoya bayansa

A daren Laraba 27 ga watan Feburairu ne shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu ya sanar da Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a karo na biyu, inda ya samu kuri’u miliyan 15.19, yayin da Atiku Abubakar ya samu miliyan 11.26.

Legit.ng ta ruwaito a jawabinsa na farko da yayi tun bayan samun nasara, Buhari ya gode ma Allah daya baiwa yan Najeriya ikon ganin wannan lokaci da aka samu cigaba a Dimukradiyyar kasa, da kuma nasarar da jam’iyyar APC ta samu.

KU KARANTA: Gumi ya shawarci Atiku ya garzaya kotu don kwatar mulki daga hannun Buhari

Nasara: Banda cin mutuncin abokan hamayya – Buhari ga magoya bayansa
Buhari da magoya bayansa
Asali: Twitter

Daga farkon jawabin nasa Buhari yace “Na gode ma miliyoyin yan Najeriya da suka sake zabena a matsayin shugaban kasarku na tsawon shekaru hudu masu zuwa, ina kaskantar da kaina tare da gode muku da kuka ga dacewar zabata na cigaba da yi muku hidima.”

Haka zalika Buharin ya kara da mika gadiyarsa ga Asiwaju Ahmad Bola Tinubu bisa gudunmuwar daya bashi, da shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomole, da kuma daraktan yakin neman zabe Rotimi Amaechi da sauran mambobin kwamitin.

Sai dai shugaba Buhari ya gargadi masoya da magoya bayansa tare da gargadinsu game da cin fuska, cin mutunci ko kuma muzguna ma abokan hamayya da kuma sauran yayan jam’iyyun adawa, musamman masu adawa da gwamnatinsa.

Buhari ya bayyana musu cewa nasarar da Allah ya basu tafi karfin duk wani kulle kulle da abokan hamayya suka shirya, kuma ta isa babban sakayya duba da irin namijin kokarin da yayi tare da masoyansa da har Allah Ya kawosu wannan matsayi.

“Ina kira ga masoya da magoya bayana dasu kada su ci fuskar abokan hamayya ko muzguna musu, nasarar da muka samu kadai ta isa sakayyar kokarin da muka yi.

“Ina kuma gode ma miliyoyin yan sa kai da duk wadanda suka bamu gudunmuwa a wannan yakin zabe da muka yi bisa sadaukar da lokacinsu da suka yi don ganin mun samu nasara, bani da isassun kalaman godiya a gareku.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel