Sabuwar gwamnatin mu za ta kara kaimi wajen tsananta tsaro, habaka tattalin arziki, yakar cin hanci da rashawa - Buhari

Sabuwar gwamnatin mu za ta kara kaimi wajen tsananta tsaro, habaka tattalin arziki, yakar cin hanci da rashawa - Buhari

Biyo bayan nasarar yayin babban zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019, shugaban kasa Muhammadu Buhari cikin jawaban sa na farin ciki ya bayyana abinda sabuwar gwamnatin sa za ta yiwa Najeriya.

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya sake jaddada daurin damarar gwamnatin sa wajen inganta tsaro, habaka tattalin arziki gami da zage dantse ta fuskar yakar cin hanci da rashawa.

Shugaban kasa Buhari ya bayyana hakan ne cikin jawaban sa na murna da kuma amincewa da nasarar sa biyo bayan babban zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar, 23, ga watan Fabrairun 2019.

Sabuwar gwamnatin mu za ta kara kaimi wajen tsananta tsaro, habaka tattalin arziki, yakar cin hanci da rashawa - Buhari
Sabuwar gwamnatin mu za ta kara kaimi wajen tsananta tsaro, habaka tattalin arziki, yakar cin hanci da rashawa - Buhari
Asali: UGC

Cikin kalami nasa, shugaban kasa Buhari ya ce sabuwar gwamnatin sa za ta kara kaimi gami tumke damarar ta wajen tsananta tsaro, habakar tattalin arziki da yakar cin hanci da rashawa.

Shugaban kasa Buhari ya ke cewa, gwamnatin za ta inganta shimfidar da ta yi a baya wajen tsarkake kasar nan daga wannan miyagun ababe domin fidda ita zuwa tudun tsira.

Yayin shan alwashi na tabbatar da hadin kan al'ummar kasar nan tare da ikirarin akidar gwamnatinsa akan rashin nuna wariya, shugaban kasa Buhari ya kuma nemi magoya bayan sa akan tabbatar da zaman lafiya ta hanyar kauracewa tunzara ko kuma takalar ‘yan adawar sa.

Kamar yadda kafar watsa labarai ta Channels TV ta ruwaito, shugaban kasa Buhari ya yi kira na neman nasarar sa ta zamto wata matashiya ta zaman lumana da kwanciyar hankali a kasar nan.

KARANTA KUMA: Sai na karbe nasara ta a hannun Buhari - Atiku

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari ya yi jinjina tare da mika godiyar sa ga dumbin al'ummar kasar nan da suka yi tururuwa wajen kada masa kuri'u da tabbatar da nasarar sa ta tazarce.

Ya kuma yabawa mambobi da jiga-jigan jam'iyyar sa ta APC da suka jajirce ba bu dare ba bu rana domin tabbatar da nasarar sa. Kazalika shugaban kasar ya kuma mika sakon sa jaje da ta'aziyya dangane da rayukan da suka salwanta yayin babban zabe da aka gudanar a makon da ya gabata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel