Sai na karbe nasara ta a hannun Buhari - Atiku

Sai na karbe nasara ta a hannun Buhari - Atiku

Mun samu cewa, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya sake jaddada matsayar sa ta rashin amincewa da sakamakon babban zabe da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta bayyana a yau Laraba.

Atiku wanda ya sha mugunyar kaye a hannun shuagban kasa Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC, ya ce ba zai amince da sakamakon babban zabe ba kuma bugu da kari zai ribaci karfin shari'a a gaban kotu wajen kwatowa kansa nasara da a cewar sa shi ya cancanta.

Sai na karbe nasara ta a hannun Buhari - Atiku
Sai na karbe nasara ta a hannun Buhari - Atiku
Asali: Facebook

Shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa, tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi furucin hakan a Yammacin yau na Laraba yayin taron manema labarai na duniya da aka gudanar cikin babban birnin kasar nan na tarayya.

Atiku cikin zayyana jawaban sa ya ce, ko kadan nasarar da Buhari ya yi kamar yadda hukumar INEC ta bayar shaida ba ya wata madogara ko manuniya da za ta haskaka muradin da marari na al'ummar kasar nan.

KARANTA KUMA: Abinda ya hana Buhari samun kuri'u 5m a jihar Kano - Ganduje

Wazirin Adamawa baya ga mika godiyar sa gami jinjina ga al'ummar kasar nan da suka yi tururuwa wajen kada kuri'u bisa ga tanadi na tabbatuwar ta 'yancin su, ya ce an gudanar da murdiya gami nau'ika na rashin gaskiya daban-daban sun yi kakagida yayin babban zaben.

Yayin misalta sakamakon zaben da almara, cikin wani rahoton mai nasaba da wannan kamar yadda shafin jaridar BBC Hausa ya ruwaito, Atiku ya ce wannan shine mafi munin zabe da ya taba aukuwa a tarihin Najeriya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel