Abinda ya hana Buhari samun kuri'u 5m a jihar Kano - Ganduje

Abinda ya hana Buhari samun kuri'u 5m a jihar Kano - Ganduje

A yau Laraba, gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya zayyana dalilai da suka sanya shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gaza samun kuri'u miliyan biyar a jihar Kano yayin babban zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar.

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Gwamna Ganduje ya ce, nuna halin ko in kula da rashin fitowa da rashin tururuwar al'umma wajen jefa kuri'u ya sanya shugaban kasa Buhari ya gaza samun kuri'u miliyan biyar a jihar Kano yayin babban zabe.

Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnan Kano gabanin babban zabe ya sha alwashin bai wa shugaban kasa Buhari kuri'u miliyan na al'ummar jihar Kano, sai kash kaddara ta rigayi fata hakan ba ta kasance ba.

Ganduje yayin kai ziyarar sa ta taya shugaba Buhari murna
Ganduje yayin kai ziyarar sa ta taya shugaba Buhari murna
Asali: Twitter

A sakamakon babban zabe da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta fitar da sanyin safiyar yau ta Laraba, shugaban kasa Buhari ya samu kimanin kuri'u 1,464,768, yayin da abokin hamayyar sa, Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 391,593 a jihar Kano.

Yayin da wasu ke hasashen murdiya da rashin adalci yayin zabe ya suka sanya Buhari ya samu wannan tarin kuri'u a jihar Kano, Gwamna Ganduje cikin mayar da martani ya misaltu a matsayin 'yan hana ruwa gudu masu adawa da dimokuradiyya.

KARANTA KUMA: Ban yarda da sakamakon zabe ba - Atiku

Da yake ganawa da manema labarai a yau cikin fadar shugaban kasa, Gwamna Ganduje ya bayyana cewa, ya yi tattaki tunda birnin Kanon Dabo domin taya shugaban kasa Buhari murna ta samun nasarar tazarce.

Duk da cewa an gudanar da zabe lami lafiya cikin kwanciyar hankali, Gwamna Ganduje ya bayyana takaicin sa dangane da yadda aka fuskanci matsaloli da suka yi tasiri wajen soke zabukan wasu yankuna cikin kananan hukumomi 17 a jihar Kano.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel