Abubuwa 10 game da Buhari bayan samun nasara

Abubuwa 10 game da Buhari bayan samun nasara

A yau Laraba, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC, ta tabbatar da nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe babban zaben kasa da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun 2019.

Abubuwa 10 game da Buhari da ya kamata ku sani
Abubuwa 10 game da Buhari da ya kamata ku sani
Asali: UGC

Shugaban kasa Buhari, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar APC, ya lallasa babban abokin adawar sa, dan takara na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, bayan da hukumar zabe ta kammala kididdiga da kidayar kuri'u da aka kada a zaben ranar Asabar.

Ga wasu muhimman ababe da suka shafi shugaban kasa Buhari da ya kamata ku sani bayan samun nasarar sa:

1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari tsohon jami'in rundunar dakarun sojin kasa ta Najeriya ne, inda ya jagorancin kasar nan a lokacin mulkin soji tsawon shekaru biyu (Daga ranar Asabar,31 ga watan Dasumban 1983 zuwa Talata, 27 ga watan Agustan 1985).

2. An yiwa lokacin mulkin Buhari lakabi da turance ake cewa Buharism, ma'ana dai lokacin da Buhari ya jagorancin kasar nan a lokacin mulkin soji.

3. Gabanin kasancewar sa shugaban kasa a shekarar 2015 da gabata, shugaban kasa Buhari ya yi takarar kujerar shugaban kasa karo uku da suka hadar da shekarar 2003, 2007 da kuma 2011 ba tare da samun nasara ba.

4. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa tarihi a shekarar 2015 inda ya ci galaba akan shugaban kasa mai ci na tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan.

5. Shugaban kasa Buhari ya kasance haifaffen 'da na 23 ga mahaifin sa, Hardo Adamu da kuma Mahaifiyar sa Zulaiha. Sai dai tarihi ya tabbatar da cewa ya taso a hannun Mahaifiyar sa bayan da ajali ya katse hanzarin mahaifin sa.

6. Buhari ya rike kujerar Gwamnan jihar Borno a lokacin mulkin soji cikin tsawon wata guda daga ranar Talata, 3 ga watan Fabrairun 1976 zuwa Litinin, 15 ga watan Maris na shekarar 1976. Ya kuma rike kujerar gwamnatin yankin Arewa maso Gabashin Najeriya tsawon watanni 7 daga ranar Juma'a, 1 ga watan Agustan 1975 zuwa ranar Talata, 3 ga watan Fabrairun 1976.

7. Buhari ya jagoranci rundunar dakarun sojin Najeriya wajen fafata yaki da dakarun sojin kasar Chadi a shekarar 1983 domin tsare iyakokin kasar nan. Rundunar Buhari ta fatattaki dakarun sojin kasar Chadi daga cikin iyaka ta kasar Najeriya.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Buhari cikin turakar sa yayin kallon yadda sakamakon zabe ke gudana

8. Shugaban kasa Buhari a lokacin jagorancin sa na mulkin soji, ya dabbaka wata doka mai tsananin gaske ta tabbatar da da'a da yiwa dokokin kasar biyayya a ranar Talata, 20 ga watan Maris na shekarar 1984.

9. Shugaban kasa Buhari ya rike jagorancin cibiyar asusun kudaden man fetur ta PTF domin tabbatar da ci gaban kasa a karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Najeriya, Marigayi Janar Sani Abacha.

10. Kyaututtuka takwas da suka rataya a wuyan shugaban kasa Buhari:

- Congo Medal (CM) Defence Service Medal (DSM)

- Defence Service Medal (Nigeria)

- General Service Medal (GSM) General Service Medal (Nigeria)

- Global Seal of Integrity (GSOI)

- Gran Collar De La Orden De La Independencia translated as Grand Collar of the Order of the Independence was conferred on Buhari by President Teodoro Obiang Nguema Mbasogo of Equatorial Guinea at the Presidential Palace on 14 March 2016

- Grand Commander of the Federal Republic of Nigeria (GCFR)

- Loyal Service and Good Conduct Medal (LSGCM) Loyal Service and Good Conduct Medal (Nigeria)

- National Service Medal (NSM)

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel